FARGABAN HARIN DAUKAN FANSA: Mazauna kwatas din Mareri a garin Gusau sun arce daga gidajen
Mazaunan kwatas din Mareri dake garin Gusau jihar Zamfara sun arce daga gidajen su a dalilin fargaban harin daukan fansa da wasu ‘yan bindiga ke shirin yi bisa dalilin kisan wani dan bindiga da aka yi a kwatas din.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES ta buga labarin yadda jami’an tsaro da suka hada da ‘yan kungiyar sa kai, ‘yan sanda da sojoji suka ceto shugaban sufuri na jihar Zamfara Aminu Adamu wanda aka fi sanin da Papa da iyalinsa daga hannun masu garkuwa da mutane.
A ranar da aka yi garkuwa da Papa, mazaunan wannan kwatas din sun yi gaggawar kiran kungiyar ‘yan sa-kai dake zama a hanyar shigowa kwatas din.
Nan da nan sai ‘yan sakan suka kira ‘yan sanda da sojoji inda suka toshe duk wata hanya da ‘yan bindigan za su iya bi su fice.
Jami’an tsaro sun kashe akalla ‘yan bindiga shida bayan sun ceto Papa da iyalinsa.
Fargaban zama a gida
Wani mazaunin kwatas din Ashafa Sani ya ce tun da abin ya faru makwabtan sa suka daina kwana a gidajen su.
Sani ya ce wasu daga cikinsu sun dawo ranar Talata amma ko da suka dawo sun shaida masa cewa baza su sake kwana a gidajen su ba idan ba sun tabbatar an samar da tsaro a kwatas din bane.
” Da na je aiki ranar Litini mai daki na ta kira ta waya cewa ta ga makwabtan mu duk sun gudu. Don in kwantar mata da hankali sai na aiki kanena ya zo ya zauna tare da su a gida saboda a ranar ba zan dawo daga wurin aiki da wuri ba.
“Da na dawo gida sai mai dakina ta ce wai wata kawarta ta ce ‘yan bindigan sun aiko da wasika cewa lallai za su dawo daukan fansar ‘yan uwan su da aka kashe.
“Ni dai ina nan a gidana tare da iyalina saboda babu wanda ke da tabbacin ko maharan za su dawo.
Wani mazaunin kwatas din Mustapha Saleem ya ce ya tattara iyalinsa sun koma zama a Tudun Wada.
“Da rana na kan shigo kwatas din domin duba gida na amma iyali na su koma zama a gidan iyaye na dake Tudun Wada.