Ƴan Najeriya sun koka a kan matsalar wutar lantarki da ta addabi ƙasar baki ɗaya

A ranar Talata ‘yan Najeriya sun koka da matsanancin rashin wutar lantarki a faɗin ƙasar nan, inda tashoshin bada wutar lantarki su ka durƙushe.

A ranar Litinin ce tashoshin bada wutar lantarki su ka durƙushe, a karo na biyu a cikin wata ɗaya.

Hakan ya haifar da jefa yawancin ƙasar nan cikin duhu, su kuma masu yin harkoki da hada-hadar ayyukan da su ka shafi aiki da wutar lantarki su ka shiga ƙaƙa-ni-ka-yi

Da rana tsaka babbar tashar bada wutar lantarki ta durƙushe a ranar Litinin, kamar yadda majiya daga kamfanonin saida wutar lantarki su ka shaida wa Premium Times.

Dama kuma a ranar 28 Ga Yuli, an samu iri wannan matsalar durƙushewar, har aka yi asarar migawats 611, kamar yadda Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN) ya bayyana.

Wani babban ɗan kasuwa mai suna Jude Okonkwo da ke harkoki a Legas, ya bayyana cewa a duk lokacin da tashar wutar lantarki ta durƙushe, to shi ma harkokin sa a ranar durƙushewa su ke yi, ya ɗibga asara mai yawa.

TCN ke kula da Babbar Tashar Raba Wutar Lantarki ta Ƙasa. Amma masana da dama sun danganta kasa bada kyakkyawar kulawa da TCN ke wa tashoshin bada wuta cewa ya jiɓinci rashin kayan aiki nagartattu na zamani ke matsalar.

Sai dai kuma a daidai wannan lokacin da tashoshin su ka durƙushe, Kamfanonin Saida Wuta (Discos) sun riƙa tura saƙonnin bada haƙuri ga kwastomomin su.

Sannan daga baya kuma aka bada sanarwar gyara matsalar, wuta ta samu a cikin ƙasa.

Ƙarshen makon jiya ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga Rahoton Musamman dangane da yadda kamfanonin sayar da wuta (Discos) su ka shafe shekaru 7 su na ɗibga asara, kuma babu isasshiyar wuta.

Tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta sayar da Hukumar Samar da Wutar Lantarki (PHCN) ga kamfanoni 11 a cikin 2013 wani Rahoton Musamman ya tabbatar da cewa gaba ɗayan su har yau babu kamfanin da ya ci riba ko ta sisin kwabo, sai ma asarar biliyoyin nairori da kowanen su ya ɗibga, kamar yadda rahotonnin Ciniki, Riba da Asara na Discos 10 ya nuna, tsakanin 2013 har zuwa 2019.

Yayin da su ka shafe shekaru kusan 9 kenan su na rabawa da sayar da wutar lantarki a Najeriya, waɗannan Discos 11 kuma sun kasa samar da hasken lantarki a Najeriya. Kenan har yau ana tafiya kamar lokacin NEPA da kuma PHCN.

Binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar da waɗannan kamfanonin sayar da wuta sun yi asarar da ta wuce naira tiriliyan ɗaya daga 2013 zuwa 2019.

10 daga cikin kamfanonin 11 sun damƙa wa hukuma rahotannin cinikin su na 2013 zuwa 2019. Kamfanin Port Harcourt Electricity Distribution Company ne kaɗai bai gabatar da na sa rahoton ba. Tuni kuma gwamnanti ke masa gargaɗin hukuntawa.

Yadda Kamfanonin Su Ka Ɗibga Asarar Kuma Su Ka Kasa Samar Da Wuta:

1. Rahoto ya tabbatar cewa Ikeja Electricity Distribution Company ne ya fi ɗibga asara har ta Naira biliyan 472 daga 2013 zuwa 2019.

2. Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ne ya zo na biyu wajen asara har ta Naira biliyan 398.9.

3. Sai na uku shi ne Kaduna KEDCO da ya yi asarar Naira biliyan 246.5.

4. Ibadan Electricity Distribution Company ya ɗibga asarar Naira biliyan 218.3

5. Mai bi masa wajen asara kuwa shi ne KEDCO na Kano da ya yi asarar Naira biliyan 202.7.

6. Enugu Electricity Distribution Company kuma ya yi asarar Naira biliyan 157.

7. Sai Eko Electricity Distribution Company da ke Legas, shi kuma Naira biliyan 151.

8. Jos Electricity Distribution Company shi ma Naira biliyan 103.1 ya yi asara.

9. Yola Electricity Distribution Company ya yi rashin Naira biliyan 81.6

10. Benin Electricity Distribution Company kuma asarar Naira biliyan 81 ta shafe shi.

Rashin Wutar Lantarki A Najeriya:

Najeriya ce ƙasar da ta fi lalacewa wajen kasa samar wa jama’a masu yawa wutar lantarki a duniya.

Har yanzu ƙarfin wutar lantarki a Najeriya bai wuce migawat 5,000 ba, alhali kuma al’ummar ƙasar sun kai mutum miliyan 200.

Sannan kuma bincike ya nuna mutum miliyan 80 ba su amfani da wutar lantaki a Najeriya.

Yayin da ƙasar Afrika ta Kudu mai yawan mutane miliyan 58, ta na samar da hasken lantarki mai ƙarfin migawat 55,000.

A waje ɗaya kamfanonin su na zargi da kuma kukan cewa Gwamnatin Tarayya ta ɗora masu harajin shigo da mita mai yawa.

A ɗaya ɓangaren kuma akwai masu cewa arha ake shan wutar lantarki a Najeriya, shi ya sa ba su samun riba.

Sai dai kuma akwai masu kafa hujjar cewa akwai dalilai na lalacewar kayan samar da wuta. Sai kuma rashin zuba jari mai ƙarfi a kasuwancin wutar lantarki. Akwai matsala ta tulin basussuka, rashin iya tafiyar da Kamfanonin rashin ingancin iya aiki.

A gefe ɗaya kuma talakawa da masu manya da ƙananan masana’antu na kukan rashin wuta da kuma saurin jan kuɗi da mitoci ke yi musamman a manyan birane.