Ƴan bindiga sun buɗawa tawagar Ganduje wuta a hanyar Zamfara

Wasu da ake zargin ƴan bindigan daji dake garkuwa mutane ne sun buɗawa ayarin motocin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a kan hanyarsu ta komawa gida jihar Kano daga jihar Zamfara.

Kamar yadda Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya tabbatar wa majiyar mu ta BBC Hausa, ya ce al’amarin ya faru ne a yau Laraba.

Sai dai majiyar ta ce Malam Muhammad ya ce harin bai shafi Gwamna Abdullahi Ganduje ba domin ba ya cikin tawagar a lokacin da lamarin ya faru, “amma ƴan bindigar sun harbi motoci biyu daga cikin ayarin.

“Sun harbi motar Hukumar Kula da kare Afkuwar Haɗurra ta ƙasa (FRSC) da ke yi wa ayarin jagora da kuma motar ɗaukar marasa lafiya da ita ma ke yi wa ayarin rakiya,” a cewar kwamishinan.

Ya ƙara da cewa duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, amma ƴan sanda uku sun ji rauni, kuma dukkansu an sallame su daga asibiti bayan duba lafiyarsu.

Gwamna Ganduje na cikin tawagar gwamnan jihar Jigawa wanda tuni ayarinsu ya yi nisa a lokacin da lamarin ya faru in ji hukumomin jihar Kanon.

“Ƴan sandan tawagar Gwamna Ganduje sun yi musayar wuta sosai da maharan inda aka fatattake su suka koma,” in ji Malam Muhammad.

Wata majiya daga gidan gwamnatin jihar Kano ta ce lamarin ya faru ne bayan da tawagar ta bar birnin Gusau daidai iyakar jihar Zamfara da ta Katsina.

Tuni dai ayarin ya isa Kano bayan faruwar lamarin.

Ayarin gwamnonin Kano da Jigawan suna komawa jihohinsu ne bayan da suka halarci taron sauya sheƙar da gwamnan Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata.