Ƴan bindiga sun babbake cibiyoyin kiwon lafiya sun yi dalilin dole aka rufe wasu 69 a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun babbake cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko biyu a karamar hukumar Batsari.

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Shamsudeen Yahaya ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a garin Katsina.

Yahaya ya ce a dalilin tabarbarewar tsaro a jihar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 69 na rufe daga cikin 1,800 din da ake da su a jihar.

“Mafi yawan cibiyoyin lafiyan dake rufe ‘uan bindigan me ke amfani da su a jihar.

“Cibiyoyin kiwon lafiyan dake kananan hukumomin Jibia, Safana, Batsari, Faskari, Sabuwa na daga cikin wadanda ‘yan bindigan ke amfani da su a jihar.

Ya ce maharan sun yi garkuwa da wasu jami’an lafiya amma sun sake su bayan wani lokaci.

“A dalilin haka ya sa jami’an lafiya da dama suka nemi a canja musu wurin aiki.

Yahaya ya ce duk da haka gwamnati ta ce za ta gyara cibiyar kiwon lafiya na matakin farko daya a kowace mazaba 361 dake jihar.

Ya ce gwamnati ta ce a shirye take ta gyara ginin tsoffin cibiyoyin lafiya dake jihar.

Yahaya ya ce gwamnati za ta dauki ma’aikata 272 domin kawar da matsalar rashin isassun ma’aikata da fannin kiwon lafiyar jihar ke fama da shi.