Ƴan bindiga sun ƙona hedikwatar karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra

‘Yan bindiga sun Kona ginin hedikwatar karamar hukumar Idemili ta Arewa dake jihar Anambra.
Maharan sun aikata haka ne da misalin karfe 2 na daren Litini.
Kotun majistare da ofishin siyar da wutar lantarki dake cikin ginin ya yi kurmus shima.
Kakakin rundunar’yan sandan jihar Tochukwu Ikenga ya ce ba a rasa rai ko daya ba sai dai asara da aka yi na ginin da abinda ke cikin sa da kuma motocin aiki da ajiye a harabar ginin.
Ikenga ya ce zuwan ‘yan sanda wurin cikin Lokaci ya taimaka wajen kashe wutar da aka yi tre da haɗin guiwar mutane dake zama a unguwar.
Idan ba a manta ba a cikin watan jiya ‘yan bindiga sun kona hedikwatar karamar hukumar Aguata dake jihar.
Sannan a ranar 31 ga Maris ‘yan bindiga sun kona hedikwatar karamar hukumar Nnewi.
Wannan shine na uku da ‘yan bindiga ke Kona hedikwatar wata karamar hukumar a jihar Anambra tun bayan da Charles Soludo ya zama gwamnan jihar.