Zulum ya jajantawa iyalan Janar Zirkushu da ƴan Boko Haram suka kashe, ya basu miliyan N20mn

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ziyarci iyalan marigayi Birgediya Janar Dzarma Zirkushu domin yi musu ta’aziyya.
Gwamnan wanda ya samu rakiyar dukkan Sanatoci uku tare da wasu ƴan majalisun tarayya daga jihar sun ziyarci iyalin mamacin a gidan sa da ke Barikin Ribadu Cantonment a Kaduna.

Zulum ya jajantawa iyalan Janar Zirkushu da ƴan Boko Haram suka kashe, ya basu miliyan N20mn
YANZU-YANZU: Kakakin Majalisa ya tura wa Ministocin Kuɗi da Ilimi sammaci kan batun tafiya yajin aikin ASUU

A yayin ziyarar, Zulum ya bada umarnin baiwa iyalan Janar Zirkushu naira miliyan N20mn kamar yadda Kakakin sa Malam Isa Gusau ya sanar. Ya kuma ce su ma iyalan sojojin da suka mutu tare da Janar ɗin za a basu nasu tallafin.
Ita ma gwamnatin jihar Kaduna ta bakin Kwamishinan ta na tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan, ta sanar da bada nata gudunmawar Naira miliyan N2mn ga iyalan mamacin.
Gwamna Zulum ya jajantawa iyalan mamacin tare da rokon su da su yi la’akari da kalaman ƙwarai da ke fitowa dava bakunan mutane akan marigayin.
Ya kuma bayyana cewa al’ummar jihar Borno ba za su taba daina godiya ga sadaukarwar da Janar Zirkushu gare su ba da sauran sojojin da suka mutu tare da shi, da ma sauran da suka rasa rayukan su a irin wannan harin da sauran da ke bakin daga.
A yayin da yake jawabin tarbon tawagar gwamnatin jihar Birno, Babban Kwamandan Sojojin barikin Ribadu Manjo Janar T. Opuene ya yaba wa gwamna Zulum da tawagarsa bisa tattaki tun daga jihar Borno zuwa Kaduna domin jajantawa iyalan mamacin. Ya bayyana Zulum a matsayin shugaban da goyon bayansa ga sojoji kasa boyuwa ga kowa.

Tura Wa Abokai

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaYANZU-YANZU: Kakakin Majalisa ya tura wa Ministocin Kuɗi da Ilimi sammaci kan batun tafiya yajin aikin ASUU

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce da ke da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jarida.