Ziyarar Atiku a Hadejia ya karfafa wa PDP guiwa a Jigawa – Dan takarar Sanatan PDP

Dan takarar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Gabas karkashin Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Nuraddeen Muhammad ya yaba ziyayar da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar ya kai ga Mai martaba Sarkin Hadejia Maimartaba Adamu Abubakar-Maje don jajanta masa da al’ummar masarautar kan ambaliyar ruwa da ya yi barna a yankin a karshen daminar bana.
Muhammad wanda tsohon Minista ne a Ma’aikatar Harkokin Waje, kuma Minista mai Kula da Ma’aikatar Watsa Labarai ta Tarayya, ya bayyana ziyarar a matsayin mai muhimmanci ga mazabarsa wadda kuma ya karfafa musu gwiwa tare da nuna cewa kasancewarsa sanata da kuma sabuwar gwamnatin PDP da suke fatar kafawa za su bayar da muhimmanci wajen magance matsalar ambaliya.
Tun farko Mai martaba Sarkin Hadejia ya bayyana Atiku a matsayin masoyin Hadejawa da kuma jihar, inda ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai su magance matsalar ambaliya da take aukuwa duk shekara.
A yayin ziyarar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa wanda ya bayar da tallafin Naira miliyan 50 don tallafa wa wadanda ambaliyar ya shafa ya jingina karuwar ambaliyar kan sauyin yanayi inda ya ce kokarin magance matsalar tare da bin hanyoyin rage dumamar yanayi ne mafita kuma shi ne abin da zai mayar da hankali inda ya zama Shugaban Kasa a Mayun 2023.
Wadanda suka rufa wa Atiku baya a yayin ziyarar sun hada da mai masaukinsa tsohon Gwamnan Jihar, Sule Lamido da Babban Daraktan Kwamitin Kamfe na Atiku/Okowa kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal da dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP Mustapha Sule Lamido da mataimakinsa Dokta Babandi Ibrahim-Gumel da shugabanni da dimbin magoya bayan jam’iyyar.
Idan za a iya tunawa Jihar Jigawa ta yi fama da ambaliya musamman a yankin Arewa maso Gabas a watab Satumban bana, inda mutum 106 suka rasa rayukansu sannan aka yi asara ta biliyoyin Naira.
Atiku ya kai irin wannan ziyara ga Mai martaba Sarkin Dutse, Mai martaba Nuhu Muhammad-Sunusi a fadarsa da ke Dutse fadar jihar.