ZAZZABIN LASSA: Dalibai biyar da malamin su daya sun mutu a makarantar almajirci a jihar Gombe

Jami’an kiwon lafiya a jihar Gombe sun bayyana cewa zazzabin Lassa ta yi ajalin dalibai biyar da malamin su daya a makarantar Almajirci dake kauyen Dogon Ruwa a karamar humumar Kaltungo.

Kodinatan hukumar cibiyar kiwon lafiya na matakin farko ta jihar Comfort Danlami ta ce ana zargin cewa mutum 76 sun kamu da cutar.

Comfort ta fadi haka ne a lokacin da jami’an ‘GoHealth’ suka ziyarci makarantar da fadar sarkin Kaltungo Sale Muhammed.

“Dalibai biyar ne suka fara kamuwa da cutar inda bayan an kai su asibiti sakamakon gwajin cutar ya tabbatar cewa zazzabin Lassa ne suka kamu da shi ba cutar sankarau ba. Sannan bayan Dan wani lokaci suka mutu.

“Daga nan sai malamin dake kula da daliban a makarantar ya kamu da cutar. Ya rasu bayan an kai shi asibiti.

Ta ce baya ga mutum 76 da ake zargin sun kamu da cutar mutim daya da aka tabbatar ya kamu da cutar na asibiti.

“Gwamnati ta kuma kebe wuri domin kula da duk wadanda suka kamu da cutar a karamar humumar.

Comfort ta ce ma’aikatan hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta aika da ma’aikata domin gudanar da bincike da gano wadanda suka kamu da cutar.

Ya Kuma ce hukumar za ta aikata da ma’aikatan ta domin wayar da kan mutanen Dogon Ruwa kan cutar da hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Abubuwan da za a kiyaye don gujewa kamuwa da Zazzabin Lassa

1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.

2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.

5. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.

6. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

7. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

8. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

9. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

10. Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

11. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.