ZARGIN BIYAN ‘YAN BINDIGA NAIRA MILIYAN 20: Rundunar Sojin Sama ta ƙaryata jaridar WSJ, ta ce masharranta ne

Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta ƙaryata labarin da jaridar World Street Journal (WSJ) ta Amurka ta buga, tare da cewa labarin ƙarya ce, sharri ne, kuma labarin bogi ne da ke nuna jaridar na yi wa harkar tsaron Najeriya maƙarƙashiya.

Jaridar WSJ a ranar Lahadi ta buga labarin cewa Rundunar Sojojin Saman Najeriya sun biya kuɗi har Naira miliyan 20 ga ‘yan bindiga a Katsina, domin karɓo fansar wata bindiga mai harbo jiragen sama da ke hannun ‘yan bindiga ɗin.

Jaridar ta buga cewa zunzurutun kuɗi naira miliyan 20 aka kai wa ‘yan bindiga har cikin Dajin Rugu, inda aka karɓo bindiga samfurin Tashi-gari-barde (Anti Aircraft Gun), AAG 12.7, wadda ake harbo jirage da ita.

WSJ ta buga cewa wata majiyar wani jami’in soja ne ya bayyana labarin ga jaridar, amma ya ce a sakaya sunan sa.

Har ila yau, WSJ ta ce Rundunar Sojojin Saman Najeriya sun biya kuɗin sun karɓo bindigar domin a cewar jaridar, sojojin sama na ganin barin bindigar a hannun ‘yan bindiga hatsarin gaske ne, domin barazana ce ga jirgin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda a lokacin an shirya zai keta hazo jihar Katsina domin zuwa jihar sa ta haihuwa.

Rahoton ya ce bayan an biya kuɗin, ‘yan bindiga sun bayar da wannan babbar bindiga, wadda nan take aka kwakkwance ta filla-filla, aka kai wani sansanin sojoji aka ajiye.

Dajin Rugu inda aka ce an kai kuɗin dai ya yi iyaka da Karamar Hukumar Batsari, Kurfi, Safana da wani yanki na jihar Zamfara.

Sai dai kuma cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar Sojojin Saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya ce labarin na bogi ne, ƙarya ce kuma sharri ne, tare da ƙoƙarin jaridar na ƙara kitsa maƙarƙashiyar dusashe nasarar da sojojin Najeriya ke samu kwanan nan wajen kakkaɓe ‘yan bindiga daga cikin dazukan jihohin Arewa maso Yamma.