ZAMFARA TA BANI TA LALACE: An kama masu safara da cin naman mutane a Gusau

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta bayyana sanarwar kama wasu mutum huɗu da ake zargi da safarar sayar da sassan jikin mutum, sai kuma wani da ya ke cin naman mutum, a Gusau, babban Jihar Zamfara.

Yayin da ake tuhumar su da laifin sayar da sassan jikin mutum, kisa da kuma cin naman mutane, wanda ke cin naman mai suna Ahmed Baba, ya shaida wa ‘yan sanda da kan sa cewa shi ya na cin naman mutum, kuma ba yau ya fara ba.

Ahmed Baba wanda magidanci ne mai ‘ya’ya 19, ya ce inda ya fi daɗi a sassan jikin mutum shi ne maƙogaro.

Kama Ahmed Baba da aka yi, ya kawo nasarar kama wasu masu safarar sassan jikin mutum su uku da Abdulshakur Muhammad, Abdullahi Buba da Ahmad Tukur.

An samu sassan mutum da su ka haɗa da hanji, maƙogaro, azzakari da idanu biyu.

“Ahmed Baba ne ya sa na samo masa sassan naman jikin mutum domin ya biya shi ladar Naira 500,000.00, kuma ya je ya samo.

Haka nan ‘yan sanda sun kama wata mata mai suna A’isha Ibrahim, wadda aka zarga da satar ɗan kishiyar ta, don ta sayar.

Kwato Bindigar Tashi-gari-barde:

Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu ya sanar da cewa ‘yan sanda sun yi arangama da ‘yan bindiga a yankunan Gumi da Bukkuyum.

A wannan artabun ne Shegu ya ce an ƙwato babbar bindiga samfurin harbo jiragen sama, wato tashi-gari-barde da wata bindiga ɗaya.

Ya ce an yi arangama sosai har ‘yan bindiga su ka ga an fi ƙarfin su, su ka shige cikin daji, su ka jefar da tashi-gari-barde a fagen yaƙi.