ZAMFARA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Mahara sun yi garkuwa da ƙanen uwargidan Abdul’aziz Yari

Bisa dukkan alamu masu garkuwa da mutane sun karkata zuwa kan manya a cikin watannin nan.

A ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:30 na dare, ‘yan bindiga sun kutsa cikin garin Talata Mafara su ka yi gaba da Auwal Husaini, ƙanen uwargidan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari.

Auwal ya shiga hannun masu garkuwa a lokacin da ya dawo daga Dubai. Kuma wanann ne karon farko da ‘yan bindiga su ka taɓa shiga cikin Talata Mafara, mahaifar tsohon gwamnan.

Wani makusancin Yari mai suna Bello Ruwan Bado ya tabbatar wa wakilin mu da wannan labari.

Auwal wanda ƙanen uwargidan Yari ne, ya zauna tsohon gidan tsohon gwamnan kafin ya yi aure.

An ce ya na da kusancin sirri sosai da Yari. Kuma majiya ta ce cune aka yi aka tafi da shi, domin ‘yan bindigar sai da su ka tambaye shi ina irin tsarabar da ya zo da ita daga Dubai?

“Sun kuma tafi da matar Surajo, maƙwaucin Auwal Husaini. Ina gida muka riƙa jin ƙarar harbi wajen 11:30 na dare.” Haka wani Mustapha ya shaida wa wakilin mu.