Zai yi wahala Amurka ta taya Najeriya dakile matsalar tsaro, saboda tabon take hakkin jama’a da ke jikin gwamnatin kasar nan – Falana

Babban Lauya kuma babban dan taratsin kare hakkin jama’a Femi Falana, ya bayyana cewa ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya daina yi wa ‘yan Najeriya romon-kunne da molon-ka, ya na sa masu ran cewa Amurka na iya sa hannu wajen taimaka wa Najeriya magance matsalolin Boko Haram da ‘yan bindiga.

“Maimakon Gwamnatin Tarayya ta rika yi wa ‘yan Najeriya molon-ka, ta na sa masu ran cewa Amurka za ta turo sojojin yaki su kare jama’ar kasar nan, to ya kamata a tilasta ita gwamnatin tarayya din ta gaggauta daukar karin sojoji da ‘yan sanda wadanda za sub kare ko’ina a cikin fadin kasar nan.” Haka Falana ya bayyana a ranar Alhamis, a Abuja lokacin da ya ke gabatar da wata takarda a wurin taro.

Falana ya gabatar da takardar wajen taron taya Farfesa Omotoye Olorode murnar cika shekaru 80 a duniya.

Farfesa Olorode, shehin malami ne fannin ilmin tsirrai da shuke-shuke da itatuwa. Sannan kuma dan taratsin kare hakkin jama’a ne.

Ganin yadda kasar nan ke kara dagulewa ne jama’a da dama ciki har da Majalisar Tarayya su ke yin kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta neman taimako daga waje, musamman Amurka.

Shikan sa Shugaba Muhammadu Buhari din a ganawar nesa-nesa da ya yi da Sakataren Harkokin Kasashen Wajen Amurka, Anthony Blinken a ranar Talata, ya roki Amurka ta duba yiwuwar kwaso sojojin ta na AFRICOM da ta girke a Stuttgart, Jamus, ta maido su cikin Afrika, wato kusa da inda ake tafka kakudubar yake-yaken tashen-tashen hankula a nahiyar.

Sannan kuma Buhari ya roki sauran kasashen duniya su goya wa Najeriya baya wajen kkarin shawo kan matsalar tsaro.

Duk da Blinken ya jaddada wa Buhari duba ywuwar abin da gwamnatin Amurka za ta iya yi, Femi Falana na ganin cewa

” Najeriya na fuskantar matsanancin rugujewar harkokin tsaro, sanadiyyar masifaffen karkatar da kudaden sayo makamai da aka rika yi daga kudaden da ake ware wa sojoji da ‘yan sanda a gwamnatoci.”

“Ba tare da Najeriya ta tuntubi kasashen Afrika ko ECOWAS ba, Shugaba Buhari ya yi azarbabin furka rokon Amurka ta maido sojojin ta na AFRICOM da ke Jamus zuwa Afrika.

Falana ya ce dan karen take hakkin dan adam da gwamnatin Najeriya ke yi ya sa Amurka da kawayen kasashen ta ba za su taimaka wa Najeriya ba, kuma shi ya sa su ka hana Najeriya manyan makaman da su ka kamata a mallaka da za a iya kakkabe Boko Haram da ‘yan bindiga da su.

“Musamman yadda ake tsare da dimbin mutane a sansanonin sojoji ba tare da an hukunta su ba, sai kuma yadda sojoji da ‘yan sanda ke karkashe fararen hula ba bisa ka’ida ba sun sa Amurka da kawayen kasashen ta ba a su taimaka wa Najeriya ba.”

Falana ya ce tun cikin 2017 Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin binciken take hakkin jama’a da ake yi, amma har yau ba a yi amfani da sakamakon binciken ba. duk kuwa da cewa tun bayan kammala bincike kwamitin ya bayar da shawarwarin matakan da za a dauka.