‘Za mu kammala aikin hanyar Numan-Gombe zuwa ƙarshen watan Disamba’- Gwamnatin Tarayya

Gwnatin Tarayya ta bayyana cewa daga nan zuwa watan Disamba ta a kammala aikin hanyar Cham zuwa Numan a jihar Adamawa da ta bayar da kwangilar sa shekarar 2017 kafin.
Kamfanin CCG na ƙasar Chine ne aka ba aikin gyaran hanyar kuma aka sakar masa Naira biliyan 9.3 a shekarar 2017 domin fara aikin, sannan a shekarar 2020 aka sake bashi ƙarin Naira biliyan 7 don kammala aikin.

‘Za mu kammala aikin hanyar Numan-Gombe zuwa ƙarshen watan Disamba’- Gwamnatin Tarayya
Dalilin da ya sa aka daina ganina a fina-finan Kannywood~ Maryam Booth

Salihu Abubakar, mai kula da aiyukan hanyoyin Gwamnatin Tarayya a jihar Adamawa, shi ne ya bayar da wannan tabbacin a garin Numan lokacin da ya kai ziyarar duba aikin, ya ce ya zuwa yanzu an kammala kilomita 20 na hanyar mai tsawon kilomita 46.
“Kuɗin kwangilar farko Naira Biliyan N9.3bn aka bayar 2017, daga bisani a shekarat 2017 Gwamnatin Tarayya ta ƙara bayar da ƙarin billion N7bn.
“Ƙarin biliyan Naira N7bn da gwamnati ta amince an bayar ne domin kula da muhimmin sashe na hanyar, wanda shine kilomita 11, wanda ya fara daga kilomita 29 zuwa kilomita 18, wanda a yanzu yana kan gabar kammaluwa, wanda ya saura bai wuce kilomita huɗu ba.
“Don haka, muna ƙira ga jama’a da su yaba da kokarin Gwamnatin Tarayya; da yardar Allah, kafin ƙarshen wannan shekarar za a kammala dukkan aikin, musamman mahimmin sashi na hanyar, ”in ji Abubakar.
Jami’in wanda ya bayyana gamsuwa da ingancin aikin, ya ce jinkirin da aka samu na aikin ya faru ne sakamakon wasu matsalolin da suka bullo a yayin aikin da suka haɗar da rashin tsaro, yankunan ruwa da kuma laka wanɗanda sun kai kilomita 11.

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 18, 2021 8:49 AM