Za a daure direbobin da suka lakadawa wani dan sanda dukan tsiya tsawon shekara biyu – Kotu

A ranar Alhamis ne rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta maka wasu direbobi biyu a kotun majistare dake Ikeja bisa laifin lakadawa dan sanda dukan tsiya.

Kotun ta kama Isiaka Toheeb mai shekara 24, Saheed Nureni mai shekara 29 da Taoheed Adeniyi mai shekara 27 da laifin hada baki da cin zarafin dan sanda a wajen aikin sa.

‘Yar sandan da ta shigar da karar, sifeto Mojirade Edeme ta bayyana cewa direbobin sun aikata haka ne ranar 26 ga Oktoba a Mile 2, Apapa.

Mojirade ta ce a haka kawai a wannan ranar Toheeb, Nureni da Adeniyi suka kaure da dambe suna cawa kansu miyagun makamai inda jin haka ya sa sifeto Egwum Sunday ya zo raba damben.

“Zuwan Sunday ya sa direbobin sun daina damben da suke yi amma ganin cewa Sunday zai kai su ofishin ‘yan sai sai suka taru tare da wasu direbobin suka yi wa dan sandan dukan tsiya.

“Rundunar ta kama mutum uku daga cikinsu amma sauran sun gudu.

Ta ce bisa ga dokar hukunta masu aikata miyagun aiyukka na shekara 2015 na jihar Legas sashe na 174 ya ce za a daure duk wanda ya ci zarafin dan sanda na tsawon shekara uku a kurkuku sannan sashe 411 na dokar ya nuna cewa za a daure wanda ya hada baki domin a ci zarafin dan sanda na tsawon shekara biyu a kurkuku.

Alkalin kotun O. A. Dirisu ta bada belin kowani direba akan Naira 200,000 tare da gabatar da shaidu biyu dake aiki kuma suke biyan gwamnatin jihar Legas haraji.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 28 ga Disemba.