ZAƁEN 2023: Ni fa a nawa ra’ayin a bar ‘yan kudu kaɗai su yi takarar shugaban kasa tunda Arewa ta yi -Inji Shekarau

Sanata Ibrahim Shekarau, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne tsawon shekaru takwas, ya bada shawarar cewa APC da ma sauran jam’iyyu har da PDP su damƙa mulki a kudancin Najeriya a zaɓen 2023.

A tattaunawa da BBC HAUSA, Shekarau ya ce tsarin karɓa-karɓa a shugabancin ƙasar nan wajibi ne. Ya ce domin ta haka ne kawai kowane yanki zai gamsu cewa an yi masa adalci a tsarin zamantakewar tafiya a ƙarƙashin dunƙulalliyar ƙasa.

Saboda haka ya ce kada na APC ta tsaya wani jinkiri ko nuƙu-nuƙu, ta bai wa ɗan kudu takarar shugabancin ƙasa kawai a zaɓen 2023.

“Tsarin rabon komai a shiyya-shiyya ba shi da hurumi a kundin tsarin mulkin Najeriya. Ana yi ne don raba-daidai. To haka shi ma karɓa-karɓa ba shi da hurumi. Sai dai ta hanyar ce kawai za a iya tabbatar da adalci idan wannan shiyyar ta karɓa, ta yi, ta miƙa wa waccan.

Shekarau ya ce kamata ya yi ‘yan Arewa su riƙa jawo ‘yan kudu a jika.

“Saboda a gaskiya idan aka karya yarjejeniyar karɓa-karɓa a zaɓen 2023, to kawuwan ‘yan Najeriya zai ƙara rabuwa.” Inji Shekarau.

A kan haka, Shekarau ya ce wannan tsari shi ne mafitar kauce wa ce-ce-ku-ce hatta ga jam’iyyar adawa, PDP.