Yunwa, Talauci da Rashin Aiki ga Matasa ke Haddasa Boko Haram -Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yunwa, talauci da rashin aikin yi ga matasa ne su ka haddasa Boko Haram kuma su ke kara ruruta wutar ta’addanci.

Haka Buhari ya bayyana a tattaunawar musamman da ya yi da Gidan Talbijin na Arise TV, ranar Alhamis, a Abuja.

“Na yi amanna gwamnati na ta yi kokari tukuru wajen yaki da Boko Haram, amma matsalar da ake ciki a yankin Arewa maso Gabas abu ne mai wuyar sha’ani.”

Ya ce ya hakakke cewa mafi yawan ‘yan Boko Haram, ‘yan Najeriya ne, kamar yadda Gwamnan Barno, Babagana Zulum ya shaida masa.

Sai dai kuma Buhari bai yi magana kan yadda malaman addini su ka assasa Boko Haram ba, ta hanyar amfani da wasu litattafan magabatan malamai, ta yadda Boko Haram sun yarda su jihadi su ke yi bil-hakki da gaskiya.

Bayan haka Shugaba Buhari ya kara da cewa kwata-kwata shi idan zai nada mukamai, to cancanta ya ke dubawa, amma ba kabilanci ko bangaranci ba.

Buhari ya yi wannan bayani a cikin wata tattaunawa da shi da aka da Gidan Talbijin na Arise TV a ranar Alhamis.

Buhari dai kusan duk lokacin da ya nada mukamai sai ya sha suka cewa ya na nuna Arewanci, bangaranci ko kabilanci.

To amma kuma a cikin wannan tattaunawar, Buhari ya ce ga dahir ya na gani mutum ya cancanta, ba zai iya tsallake shi ya saki reshe ya kama ganye ba.

Saboda haka Buhari ya ce cancanta ya ke bi ba kabila ba.

Duk da haka akwai masu ganin cewa Buhari ba ya bin abin da dokar kasa ta ce, wato a raba mukamai ba tare da wani yanki ya yi korafin an maida ahi saniyar-ware ba.

Da ya ke magana kan mukamai, ya ce ba zai iya yin alfarma ga wadanda ba su dade a aiki ba, alhali ga wadanda su ka dade su na aikin.

“Mutane da yawa sun shafe ahekaru da yawa su na samun horo. Wasu sun yi shekaru 18, wasu fiye da 10. Sun samu horo a Zaria da Abeokuta. Sun bi matakan aikin soja mukamai daki-daki. To kuma ka na da irin wadannan kwararru kuma gogaggu, sai ka tsallake su ka dauko wani can da bai dade ba, bai kuma goge ba, don kawai a ga ka na raba-daidai a mukamai?” Inji Buhari.

Buhari na magana ne a kan nada sabon Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Yahaya Faruk.

Na Nada Yahaya Sabon Babban Hafsan Sojoji Saboda Ya Fi Sanin Dabarun Yaki, Kuma Dakaru Na Goyon Bayan Sa -Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya kare dalilan sa na nada Manjo Janar Yahaya Faruk Sabon Babban Hafsan Askarawan Najeriya, bayan rasuwar Janar Ibrahim Attahiru.

Cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Talbijin na Arise TV a ranar Alhamis, ya kare zargin da ake yi masa cewa ya na nuna kabilanci ko bangaranci wajen nade-naden mukamai.

Buhari ya ce shi cancanta da kwarewa ya ke bi, ba Arewanci ko kabilanci da bangaranci ba.

Da ya ke magana kan kan Sabon Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Buhari ya ce ya nada Yahaya Faruk saboda ya dade a fagen yaki da Boko Haram, kuma dakarun da ke bakin daga su na ba shi goyon baya dari-bisa-dari.