Yaushe gwamnatin Zamfara za ta biya kudaden Jarabawar NECO wa daliban jihar? Daga Abba Tsafe

Gwamnatin Jihar Zamfara tana daya daga cikin jihohi mafi ci baya a bangaren ilmi saboda sakacin da gwamnatin Matawalle ke yi da harkar ilmin.

A wannan gwamnatin babu wani ci gaba da ake samu, kullun al’amarin ilimin jihar Zamfara sai kara tabarbarewa yake yi. Daga shekarar 2014 ne dalibai a Zamfara suka san a saki sakamakon jarabawa amma ba’a biya kudi ba, har yanzu da nake wannan rubutu babu wani bayani mai gamsarwa game da jarabawar NECO/WAEC.

Shin nawa ne kudin jarabawar da har za su gagari gwamnati biya? idan muka lura da makudan kudaden da gwamnati take kashewa a wajan wasu ababen da basu da wani amfani ga ci gaban jihar, kawai dai a fili yake cewa gwamnatin ba ta damu da harkar ilmi ba.

Duk lokacin da akace jarabawar WAEC ko NECO ta fito zakaga yayan masu hannu da shuni sunata rigwangwoniya wajen duba sakamakonsu, amma yayan talakawa a Zamfara saidai kaji suna fadar cewa mu ko sai yaushe Gwamnati zata biya kudinmu?

Saboda haka Gwamnati taji tsoron Allah ta tausayawa yayan talakawa dake karatu a makarantun gwamnati ta rika biyan kudin jarabawarsu akan lokaci domin suma su shiga tsara wajen zuwa makarantun gaba ga secondary; yin hakan zai taimaka sosai wajen magance matsalar tsaron da Jihar Zamfara ke fama dashi da kuma shan miyagun kwayoyi da matasa suke fama dashi.

A tausaya wa ‘ya’yan Talakawa

A gefe daya ‘Ya’yan talakawa yan asalin jahar Zamfara suna cikin jimami, tunani tare da tagumi a gidajen iyayensu a sakamakon yadda suke ganin takwarorinsu Yayan masu hali dake makarantu masu zaman kansu, ke ta faman shirye shiryen wucewa jami’o’i da sauran manyan makarantu saboda sakamakon jarabawar su yayi kyau kuma an biya masu.

Sama da shekaru kenan daliban jahar Zamfara suke rasa damar da suke dashi na shiga manyan makarantu a cikin lokaci wanda wasu ma sun watsarda karatun a sakamakon rashin biyan Kudaden jarabawar da gwamnatin jahar Zamfara keyi, ko da kuwa anbiya za a biya ne daga bayan alkalami da kwakwalwar yara ta dallashe.

Idan muka yi la’akari da can baya gwamnatin jihar Zamfara ba ta wasa da jarabawar, tana biya a cikin lokuttan da ya kamata kama daga 2010,2011,2012.

Haka kuma sauran jihohi da muka samu ‘yanci tare dasu sun cigaba matuka ta a harkar ilimi, Don haka ya kamata muma a shawo kan wannan matsala wadda taki ci taki chanyewa.

Muna kira da babbar murya ga gwamnati da ta tausaya wa daliban nan ta biya wadannan kudade domin ci gaban karatun kannen mu.

Daga karshe ina rokon Allah ya taimaki jahar Zamfara, Allah ya yi ma gwamnan jahar Zamfara jagoranci a cikin mulkin sa

Rubutawa
Abba Bala Haruna Tsafe
08167015160