Yarbanci ba ya cikin harsunan da kasar Brazil ke amfani da su a hukumance – Binciken DUBAWA

Zargi: Wata jarida da wadansu shafukan sada zumunta na zargin wai Brazil ta fara amfani da harshen yarbanci a matsayin daya daga cikin harsunan da kasar ke amfani da su a hukumance kuma wai har za ta fara amfani da harshen wajen koyarwa a makarantun firmare da na sakandare

Wata jarida da wasu shafuka da dama sun rubuta labaran da aka yi ta yayatawa a soshiyal mediya game da zargiin wai Brazil ta fara amfani da yarbanci a matsayin daya daga cikin mahimman harsunan kasar. Haka nan kuma wai gwamnatin kasar ta tilasta karatun tarihin Afirka da harshen yarbanci a makarantun firamare da sakandare.

Labaran sun bayyana majiyarsu a matsayin ministan al’adun Brazil Dr Sergio Sa Leitao

Ranar juma’a 12 ga watan Nuwamba jaridar Independent ta wallafa labarin da ta yi ma taken “Harshen Yarbanci ya zama daya daga cikin harsunan da ke kan gaba a duniya tunda yanzu ya zama tilas a yi amfani da shi a makarantun firamare da sakandare a Brazil.

EagleForeSight, wani shafi a yanar gizo shi ma ya wallafa labarin ranar 11 ga watan Nuwamba yana cewa “Labari da dumi-dumi Brazil ta fara amfani da yarbanci a matsayin daya daga cikin mahimman harsinan kasar”

A cewar wadannan labaran, ministan al’adun, wanda ya yi jawabi a jami’ar Sao Paulo ya ce: Mun sanya tarihin Afirka da harshen yarbanci a makarantun ne dan muna fata zai taimaka wajen kawo kusanci tsakanin ‘yan Afirkan Brazil da tushensu, kuma ta yin hankan zai inganta fahimtan harshen da sauran harsuna masu mahimmanci da ke Brazil banda Portuganci wanda shi ne harshen da kowa ke amfani da shi.

Tantancewa
Dubawa ta fara lura da cewa labaran da aka yi ta yayatawa a yanar gizo iri daya ne kuma yawancinsu sun bayyana majiyarsu a matsayin ministan al’adu na Brazil Dr, Sergio Sa Leitao.

Daga nan sai Dubawa ta yi binciken kalmomi na musamman a shafin google inda ta gano cewa labarin ma ba sabo ba ne, an riga an yi ta yayata shi tun shekarar 2018 a wasu shafukan yanar gizo.

A shekarar 2019, kamfanin dillancin labaraban Faransa AFP ya yi wani rahoto sadda batun ya fara bulla. A rahoton ya ambaci Dr Sergio Sa Leitao a matsayin tsohon ministan al’adu.

Dubawa ta cigaba da bincike dan gano dalilin hakan inda ta fahimci cewa shugaban kasa, Jair Bolsonaro ya rusa ma’aikatar al’adun a watan Janairun 2019. A cewar rahoton na AFP. Wani mai magana da yawun sakataren al’adu na musamman a Brazil ya ce tsohon mnistan bai taba amabatan irin wadannan kalaman ba.

Domin tantance wannan batu dubawa ta tuntubi ma’aikatar kula da dangantaka da kasashen ketare, kuma tana jira ta ji daga wajen su. Wani dan jaridan Brazil, Pedro Kutney ya ce yarbanci bai taba kasancewa daya daga cikin manyan harsunan Brazil ba, Portuganci ne kadai ake amfani da shi.

Ya kuma cigaba da yin karin bayani kamar haka: “Brazil na daya daga cikin kasasjen da ta karbi mafi yawan bayin da aka kawo daga nahiyar Afirka, kusan milliyan 5.8 cikin miliyan 12.5 din da aka yi fataucinsu daga Afirka zuwa Amirka. A Brazil an yi cinikin bakake daga shekarar 1535 zuwa 1888 kuma babu shakka mafi yawan al’adun kasar daga Afirka aka kawo.

Daya daga cikinsu shi ne addini da kuma irin tsafin da yarbawa ke yi. Musamman a Bahia jihar da ta fi yawan bakaken fata, yawancinsu na amfani da kalmomin yarbanci kuma shi ne harshen da malaman addini ke amfani da shi wajen tsafi, “dan haka yarbanci wani bangare ne na tarihi da al’adar Brazil. Doka ta amince da shi a manyan birane biyu, wadanda su ka hada da Rio de Janeiro da Salbador amma ba’a taba daukar shi a hukumance a kasar baki daya ba.”

Wani dan jarida mai suna Kaike Nanne ya kwatanta labarin a matsayin “fake News.” “Wannan fake news ne. Babu yadda yarbanci zai maye gurbin portuganci. Ana amfani da shi a wasu al’ummomin bakaken fata da kuma kungiyoyin Candomble shi ke nan.”

Wani harshe Brazil ke amfani da shi a hukumance
Portuganci ne Brazil ke amfani da shi a hukumance kuma shi ne harshen da kusan kowa ke amfani da shi a kasar, a cewar world population review akwai harsuna 228 a Brazil wadanda suka hada da Portuganci da wasu harsuna 11 wadanda baki suka kawo sai kuma wadansu 217 na ‘yan asalin kasar.

A karshe
Zargin wai Brazil za ta fara amfani da yarbanci a makarantun firamare da sakandar ba gaskiya ba ne. Abin da aka wallafa a shafukan yanar gizo tsohon labari ne aka dawo da shi ana yayatawa.