Yanzu Tanko Yakasai ba tsohon ɗan siyasa ba ne, tsohon da keman agaji ne kawai – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta fito ta caccaki dattijo Tanko Yakasai saboda shakkun da ya ce ya ke da shi dangane da goyon bayan da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke da shi da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu.
CIkin wata sanarwa da Kakakin Fadar Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya ce ai ba wanda ya san akwai ma wani wai shi Tanko Yakasai a cikin APC.
Shehu ya ce Yakasai ba shi da wani tasiri a cikin APC, kuma goyon bayan da ya ke nuna wa Bola Tinubu ba shi da wani karsashin da zai ƙara wa Jagaban komai.
“Ba wanda ya san Alhaji Tanko Yakasai a cikin APC. Amma kowa na da ‘yancin bayyana ra’ayin sa. Abin da ya bayyana a cikin tattaunawar da aka yi da shi a baya-bayan nan, ra’ayin sa ne ba na APC ko tawagar Shugaban Ƙasa ba. Ana maraba da goyon bayan da ya ke bai wa Bola Tinubu, amma fa da wahala a iya ganewa ko ganin irin tasirin da goyon bayan na sa ke ƙara wa Tinubu ɗin.”
Shehu ya ce iƙirarin da Yakasai ya yi kan tababar sa ga goyon bayan da Buhari ke bai wa takardar Tinubu, kwata-kwata babu gaskiya a cikin bayanan sa.
Ya ce Tanko Yakasai ya shafto magana kawai maras tushe, makama ko hujja. Don haka ya ƙara da cewa kada wanda ya ɗauki maganganun dattijon a matsayin gaskiya.
“Iƙirarin Yakasai kan rashin goyon bayan Tinubu da ya yi zargin Buhari ba ya yi, ba gaskiya ba ce. A ranar Litinin ɗin nan fa Shugaba Buhari ya je Bauchi ya yi wa Tinubu kamfen. Kuma duk da irin ayyukan da ke gaban sa na mulkin ƙasa, cikin makonni masu zuwa zai ƙara zuwa wasu jihohin ya taya shi kamfen.” Inji Shehu.
“Amma fa a kula da cewa wannan dattijon neman agaji ko tallafi kawai ya ke yi, ba wani abu ba,” inji Shehu.
Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ce aka yi hira da Yakasai a gidan talabijin na Control TV, inda ya ce a jikin sa ya na jin Shugaba Buhari ba ya goyon bayan takarar Tinubu.
Ya ce ya na ganin irin ɗabi’u da kamannun Tinubu ba su faranta wa Buhari rai.