‘Yan sanda sun rufe kasuwar Mammy dake a jihar Yobe saboda fargabar tashin Bam

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta rufe kasuwar Mammy dake cikin barikin ‘yan sanda a Damaturu.
Mammy kasuwace dake da gidajen siyar da giya dama a barikin sojoji ko na ‘yan sanda.
Rundunar ta ce ta yi haka ne domin kare kanta ganin yadda Boko Haram da ISWAP ke dasa bama-bamai a gidajen siyar da giya a jihar.
Idan ba a manta ba a ranar Larabar da ta gabata PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda mutum shida suka mutu bayan Boko Haram sun tada bamabamai a Geidam da Gashua.