Yan sanda sun kama mutumin da ya kashe matarsa don ya mallaki makarantar da suka bude tare

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani magidanci mai shekara 45 Segun Omotosho da ake zargi da kashe matarsa Olubukola Omotosho da dukan tsiya saboda ya mallaki makarantar da suke buɗe.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya sanar da haka a wata takarda da ranar Litinin a garin Abeokuta.
Oyeyemi ya ce rundunar ta gano cewa Olubukola wacce ke da satifiket a harkar koyarwa ta bude makarantar boko da sunan ta tare da mijinta.
Ya ce mijin Omotosho kafinta sannan kullum ya dawo gida sai ya kama ta da duka kawai domin wai dole ta mallaka masa makarantar da ta bude.
Oyeyemi ya ce a ranar da Omotosho ya yi wa matarsa duka na ƙarshe Omotosho ya kwada wa shirgegen kwadon kofa inda hakan yasa ta fadi sume.
“Da Omotosho ya samu labarin rasuwar matarsa sai ya gudu ya bar garin.
“Bayan jami’an tsaron sun kamo shi aka saka masa rikodin din da matarsa ta yi ta aika wa ‘yan uwanta kafin ta rasu.
“A rikodin din Olubukola ta ce ‘yan uwanta su kama Omotosho saboda shine yayi ajalinta. Ta ce Omotosho ya kwada mata wani shigen kwado a kai bayan duka da ya lakada mata.
Oyeyemi ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka za ta ci gaba da gudanar da bincike akai domin hukunta shi.