‘Yan sanda sun damke dan shekara 30 din da ya nemi yi wa dattijiya mai shekaru 75 fyade

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama Sunday Nwadiagha mai shekara 30 da laifin yi wa tsohuwa mai shekaru 75 fyade.
Kakakin rundunar Tochukwu Ikenga wanda ya sanar da haka ranar Asabar a garin Awka ya ce rundunar ta kama Nwadiagha wanda shi dan asalin kauyen Eyiba jihar Ebonyi a kauyen Nkwelle Awkuzu da misalin karfe hudu na yamma.
Ikenga ya ce jami’an tsaron sun kama Nwadiagha a gonar wannan tsohuwa dake Nkwelle Awkuzu a daidai yana kokarin aikata wannan mummunar abu.
“Jami’an tsaron sun kama Nwadiagha a dalilin ihun da tsohuwar ta yi a lokacin.
“Ihun da ta yi ya jawo hankalin mutane inda suka zo suka cece tsohuwar kuma suka lakada wa mutumin dukan tsaya sannan suka hada shi da ‘yan sanda.
Ikenga ya ce rundunar ta kai tsohuwar da Nwadiagha domin likita ya duba su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Echeng Echeng ya yi kira ga mutane da su daina dauka doka a hannun su a duk lokacin da suka kama mai laifi.
Echeng ya ce rashin daukan doka a hannu na taimaka wa jami’an tsaro gudanar da bincike yadda za a iya hukunta duk mai laifi bisa ga doka