‘Yan Boko Haram ɗin da su ka yi saranda sun nemi sauran kangararrun su fito su miƙa wuya

Wasu tubabbun ‘yan Boko Haram sun yi da-na-sanin shigar su ayyukan ta’addancin kashe mutane da ɓarnata dukiyoyin al’umma a Arewa maso Gabas.

Sun yi wannan bayani a lokacin da ake kewayawa da manema labarai, domin su ga ɗaya daga cikin wuraren da ake killace ‘yan ta’addar da su ka miƙa wuya ana yi masu huɗubobi, wa’azi da nasihohin wankin ƙwaƙwalwar kankare masu mummunar aƙidar ta’addanci a zukatan su.

An dai gudanar da wannan rsngadi da ‘yan jarida ne a ranar Talata a Barno.

Ɗaya daga cikin waɗanda su ka yi jawabi a cikin tubabbun ‘yan Boko Haram ɗin ya ce kwamandojin su sun yaudare su, domin ba su faɗa masu gaskiyar dalilin da ya sa aka ɗauke su ayyukan ta’addancin ba.

Ya ce sannan kuma sun fahimci ba za su iya ci gaba da mummunar rayuwar da su ke yi a cikin daji ba.

Sannan kuma ya nuna cewa sun yanke shawarar yin saranda su watsar da ayyukan ta’addanci saboda sojoji sun yi masu zobe, babu wurin gudu a tsira a cikin dazukan.

Sannan kuma ya nuna cewa tun tuni su ka so yin saranda, amma sun jinkirta ne saboda tsoron kada su fito sojoji su kama su, su karkashe su.

Ya ƙara da cewa fitowa a yi saranda a miƙa wuya ga sojojin Najeriya shi ne abu mafi kyau. Don haka ya roƙi sauran kangararrun da ba su miƙa wuya ba cewa su fito su yi saranda kawai.

“A da can mun ji tsoron kada mu ajiye makamai mu fito a kama mu a kashe. Amma a gaskiya ba haka ba ne. Ga shi mun yi saranda kuma ana kula da mu a cikin mutunci ba a tozarta mu.

“Ina kira ga abokan mu da mu ka yi wannan abu a baya, su ma su fito su yi saranda. Saboda za a karɓe su a cikin mutunci, ba tare da ƙasƙanci ba.”

Ya ce ya shafe shekaru shida ya na yaƙi a cikin ‘yan Boko Haram. Amma daga baya dai ya ce ya fahimci babu riba a duniya, sannan babu riba a lahira.

Kwamandan Zaratan Sojojin Musamman na Runduna ta 21 a Bama, Adewale Adekeye, daga watan Yuli zuwa yanzu an karɓi dubban ‘yan Boko Haram tare da iyalan su da su ka miƙa wuya, su ka yi saranda.

Ya kuma ce ya fahimci irin fargaba da tsoron da zaman ɗar-ɗar ɗin da jama’a ke yi su na nuna rashin gamsuwa sosai da shirin gwamnati na karɓar tubabbun Boko Haram.

Ya ce wannan shiri ba baƙo ba ne a tarihin yaƙe-yaƙe a duniya. Domin hakan maslaha ce ta wanzar da zaman lafiya.

Ya ce ba aikin sojoji ba ne su kashe waɗanda su ka yi saranda.

“Mu ake fara tunkara da waɗanda su ka yi saranda. Mu kuma aikin mu ne mu karɓe su mu tantance su.

“An fi yin wannan aikin killace waɗanda su ka yi saranda nan a Ƙaramar Hukumar Bama, saboda a cikin ta ne wawakeken dajin Sambisa mai faɗi ya fi yawa.”