‘Yan bindiga sun sako mutum 10 cikin 13n ma’aikatan karamar hukumar Zariya da suka sace a Giwa

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya sanar da sakin ma’aikatan karamar hukumar Zariya da ‘yan bindiga suka yi a cikin farkon wannan wata.

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ‘yan bindiga sun yi awaon gaba da wasu ma’aikatan karamar humar Zariya a hanyarsu ta zuwa ta’aziyyar rasuwar mahaifin abokin aikin su dake karamar hukumar Giwa.

Wasu daga cikin ‘Yan uwan wadanda aka sace da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labarai a Zariya, sun ce maharan sun bukaci a aika musu da naira miliyan 40 da sabbin babura 3 kafin su saki wadanda suka yi garkuwa da su.

” Sun bukaci a aika musu da naira miliyan 40 da babura sabbi 3. Yan uwa da abokan arziki suka hadu aka yi karo-karo a tara kudin a ka kai musu. sai dai ba a kai da babura uku da suka ce ba shi yasa ba a sako mutum uku cikin wadanda aka sace ba sai suka sako mutum 10.