‘Yan bindiga sun saki faston cocin Katolika da suka sace bayan an biya miliyoyin naira kuɗin fansa

Shugaban kwamitin gudanarwa na cocin Katolika dake jihar Akwa-Ibom Cletus Okodi ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun saki faston cocin St Pius dake kauyen Ikot Abasi Akpan, a karamar hukumar Mkpat Enin Alphonsus Uboh bayan ya yi kwanaki hudu tsare a hannun maharan.
‘Yan bindigan sun yi garkuwa da Uboh ranar Lahadi a cikin gidan sa dake cikin haeavar cocin da misalin karfe bakwai na yamma.
Maharan sun bukaci a biya su kudin fansan Naira miliyan 100 kafin su sake shi.
Okodi ya tabbatar cewa sai da coci ta biya kudin fansar kafin maharan suka saki faston sai dai bai fadi ko nawa bane kudaden da suka biya maharan ba.
“Mun biya ‘yan bindigan kudi kafin suka saki Uboh sai dai kudin da muka biya ba su kai naira miliyan 100 din da maharan suka bukata ba, sun ɗan rage mana bayan mun taya.
Yin garkuwa da Uboh shine karo na biyu da mahara ke yi a jihar a cikin makonni uku da suka wuce.
Masu garkuwa sun yi garkuwa da faston cocin Solid Rock John Okoriko makonin biyu da suka gabata.Maharan sun bukaci a biya naira miliyan 100 kafin su sake shi shima.
Bayan haka wani faston cocin Katolika a jihar Kaduna da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a kwanakin baya ya rasu a hannun maharan.
Cocin Katolika na jihar Kaduna ta ce fasto Joseph Bako ya rasu tsakanin ranakun 18 zuwa 20 ga Afrilu.
Bako ya rasu yana da shekara 48 a duniya.