‘Yan bindiga sun kai hari wasu coci biyu, sun kashe mutum uku, sun yi garkuwa da mutane da dama daga Kaduna

A ranar Lahadi ne Kwamishinan Tsaron Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu coci biyu inda suka kashe mutum uku, biyu sun ji rauni sannan suka yi garkuwa da mutane da dama a kauyukan karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Aruwan ya ce bisa ga rahoton da gwamnati ta samu daga wajen jami’an tsaro ya nuna cewa maharan sun far wa kauyukan Ungwan Fada, Ungwan Turawa da Ungwan Makama dake Rubu duk a karamar hukumar Kajuru ranar Lahadi.
Ya ce maharan sun fara kai hari a kauyen Ungwan Fada sannan suka gangaro zuwa Ungwan Turawa da Ungwan Makama sannan suka afka kauyen Rubu.
A kauyen Rubu maharan sun kai hari cocin Maranatha Baptist da cocin Katolika na St. Moses.
Mutum uku sun mutu sannan wasu mutum biyu da suka hada da mace da namiji sun ji rauni.
‘Yan bindigan sun yi garkuwa da mutane da ba a san yawan su ba daga kauyukan sannan sun sace kayan masarufi bayan sun kutsa shagunan mutane da abinci.
Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Hadiza Balarabe ta yi tir da harin da ‘yan bindigan suka kai sannan mika sakon ta’aziya ga iyalai da da yan uwan wadanda suka rasa rayukan su.