YAJIN AIKIN MALAMAN JAMI’O’I: ASUU ta ƙara maƙonni 8 kafin ta sake waiwayen Gwamnatin Tarayya, ta ce ‘gwamnatin maƙaryata’ ce

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta bayyana ci gaba da yajin aiki har ƙarin tsawon watanni biyu nan gaba, kafin ta sake waiwayar Gwamnatin Tarayya.

Shugabannin ASUU sun kwana taro a Hedikwatar su da ke Jami’ar Abuja, wanda su ka fara tun daga ranar Lahadi, har zuwa wayewar garin yau Litinin.

Wata majiya daga cikin mahalarta taron ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa tabbas sun kwana taro, kuma sun yanke shawarar cewa za su ci gaba da yajin aiki, tunda gwamnatin tarayya ta ɗauke su sakarkaru.

Majiyar wadda ta ce kada a ambaci sunan ta, ta ce za su ci gaba da jayin aiki har sai sun nuna wa gwamnatin tarayya cewa lallai ta watsar da ilmi a ƙasar nan, ta bar shi ya na neman lalacewa.

Majiyar ta ce yanzu haka ana nan ana rubuta takardar bayan taro wadda za a raba wa manema labarai.

Malaman inji majiyar sun zargi Gwamnatin Tarayya da rashin cika alƙawari, yin baki biyu da kuma zumbuɗa ƙarya.

A baya dai bayan gwamnati ta sha yi wa ASUU alƙawari, kwanan baya Gwamnatin Tarayya ta fito ta ce ba ta da kuɗaɗen da za ta iya biyan buƙatun malaman jami’o’i.

Dama kuma watanni biyu baya ASUU ta ce idan sun sake tafiya yajin aiki, to a tuhumi Buhari, gwamantin sa ce ta kasa cika masu alƙawari ko da guda ɗaya.