Yadda ‘Yan bindiga suka kashe mutum 12 a harin Zangon Kataf, Jihar Kaduna

A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 12 sannan wasu mutum biyu sun ji rauni a harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyukan karamar hukumar Zangon Kataf.

Kwamishinan Tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya sanar da haka a garin Kaduna.

Aruwan ya ce jami’an tsaro sun shaida wa gwamnati cewa maharan sun far wa kauyen Peigyim dake kusa da Kibori a masarautar Atyap ranar Lahadi da yamma ne.

“Maharan sun kashe akalla mutum 12 sannan mutum 2 sun ji rauni.

Aruwan ya ce gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya aika da sakon ta’aziyarsa ga mazaunan kauyen Peigyim sannan ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankulansu.

Ya ce jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike domin kamo wadanda ke da hannu a tada rikici a yanki.

Jihar Kaduna na cikin jihohin yankin Arewacin Najeriya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Sannan kuma har ila yau ‘yan bindiga sun kashe wani faston cocin ‘Evangelical Church Winning All (ECWA)’ Reverend Silas Ali wannan karamar hukuma ta Zangon Kataf.

Aruwan ya ce kafin Ali ya rasu shine babban faston cocin ECWA dake kauyen Kibori-Asha Awuce, a karamar hukumar Zangon Kataf.

“Ali ya gamu da ajalinsa ranar Asabar a hanyarsa ta zuwa Kafancan inda kafin ya yi nisa mahara suka tare motar a kauyen Kibori kusa da Asha-Awuce suka kashe shi.