Yadda rundunar sojin sama suka kashe fitaccen dan bindiga, matan sa biyu da kwamandojinsa 8 a Katsina

A wani luguden bamabamai da sojojin saman Najeriya suka yi a cikin makon jiya sun samu nasarar gamawa da wani fitattcen dan bindiga da ya buwayi mutane a jihar Zamfara mai suna Abdulkarimu da aka fi sanin sa da Faca-Faca, matan sa biyu da manyan kwamandojinsa 8.
Rundunar ta kai wa Faca-Faca hari a kauyen Marina dake karamar hukumar Safana jihar Katsina da misalin karfe 3 na daren Lahadi.
PREMIUM TIMES ta tattaro bayanan harin da rundunar sojin saman ta Yi daga wajen majiya dake
Majiyar da PREMIUM TIMES ta samo wadannan bayanai ‘Forward Operation Base (FOB)’ ta bayyana cewa jami’an tsaron sun kai wa Faca-Faca hari bayan samun bayanan siri game da inda yake kwana.
kakakin rundunar Gambo Isa ya tabbatar da harin inda ya ce “Rundunar sojin sama sun kashe mutum takwas da ake zargi ‘yan bindiga ne da shugaban su Faca-Faca. Wasu daga cikin maharan sun gudu.
Dan majalisar dokokin jihar AbdulJalal Runka ya tabbatar da aukuwar wannan aiki da sojoji suka yi.
Sannan wasu mazaunan Safana su biyu sun bayyan wa PREMIUM TIMES cewa mutane da dama sun gudu sun bar gidajen su a dalilin wannan farmaki kan yan bindiga da sojoji suka kai.
Faca-Faca
Wani mazaunin Safana Shamsu Masud ya ce Faca-Faca ya dade yana kawo wa kauyukan dake karkashin kananan hukumomin Safana, Danmusa, Batsari da wasu bangarorin jihar Zamfara hari.