Yadda kotu ta ci tarar ɓarayin ɗanyen man naira miliyan 200 tarar naira dubu 20, aka sallame su

Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya ta Warri, da ke Jihar Delta, Okon Abang, ya yanke hukuncin da ran sa bai so ba ko kaɗan, amma kuma babu yadda zai yi.

Abang ya yanke wa mutum 9 da ya samu da laifin satar ɗanyen mai suka loda a jirgin ruwa, har na naira miliyan 200, hukuncin biyan tarar naira 2,000 kowanen su.

Sannan kuma aka ci su tarar naira miliyan biyar kuɗin fansar jirgin ruwan su na dakon ɗanyen mai wanda aka kama su tare.

Mutanen dai an kama su ne a ranar 11 Ga Nuwamba 2015, lokacin da Sojojin Ruwan Najeriya ke sintiri. An kama su a cikin jirgin ruwan da suka saci ɗanyen man su ka loda.

Sojojin Ruwan Najeriya ne su ka kama su, sannan su ka damƙa su ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

Bayan an tsananta bincike, an gano mutanen sun daɗe su na satar ɗanyen man Najeriya.

Daga nan kuma Ofishin Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya karɓe binciken, inda a ranar 8 Ga Afrilu, 2016 aka gurfanar da mutum 9 a cikin mutum 13 da aka kama, aka saki mutum uku.

Mai Gabatar Da Ƙara Ta Koma Gabatar Da Shiririta:

An fara shari’a tiryan-tiryan Amma daga baya, sai mai gabatar da ƙara daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya, Onyeka Ohakwe ta shigar da sanarwar yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin waɗanda ake tuhumar da kuma Gwamnatin Tarayya, wato ‘plea bargain’.

A tsarin ‘plea bargain’, ɓarawon kayan gwamnati zai ajiye kayan da ya sata, ko ya biya kuɗin da ya wawura, sannan a yi masa sassaucin hukunci.

Yayin da aka zo yanke hukunci, Mai Gabatar da ƙara a ranar 27 Ga Oktoba, 2021 ta shaida wa kotu cewa ai an yi yarjejeniyar ‘plea bargain’ da ɓarayin su da gwamnati. Wato hakan na nufin tilas kotu ta yi masu sassauci kenan wajen yanke masu hukunci.

Yadda Mai Gabatar Da Ƙara Ya Rufta Mai Shari’a Cikin Rijiya:

Jikin Mai Shari’a Okon Abang ya yi sanyi laƙwas, ganin yadda aka nunke shi baibai, ta yadda zai jingine tsatstsauran hukuncin da ya yi niyyar danƙara ɓarayin, wanda zai iya kai shekaru masu yawan da sai sun mutu a kurkuku kafin wa’adin fitar su ya cika.

Abang da ya karanta sabon cajin da ake wa ɓarayin, zuciyar sa ta ɓaci, amma babu yadda ya iya, tunda alƙali na yanke hukunci ne bisa duba da irin tuhumar da mai gabatar da ƙara ya gabatar masa.

“Wannan wace irin yarjejeniya ce kuma babu daɗin ji ko kaɗan? Maimakon a ƙara tsaurara masu tuhuma, sai a sassauta?

“Irin waɗannan mutanen fa kamata ya yi a ɗaure su har igiya ta yi rara, ba a sassauta masu tuhuma su ci bilis ba.” Inji Mai Shari’a Abang.”

Abang dai ya yanke masu hukuncin tarar naira 2,000 kowanen su mutum 9. Sai jirgin ruwan na su wanda a shari’a ƙwace shi ya kamata a yi, amma sai aka ce su biya tarar naira miliyan 5 kacal a sakar masu jirgin su.

‘Banza Ta Kori Wofi: Ɓarayin Da Gwamnati Ta Yi Wa Gata A Kotu, Ba Da Son Ran Mai Shari’a Ba:

Ɓarayin ɗanyen man har metric tan 4,000 sun haɗa da:Adeola Goodness, Olaoluwa Temitope, Kelvin Onyeka, Dare Likman, Ibrahim Sese, Amaechi Nkwocha, Anayo Chukwu, Emmanual Ekwuma da Lucky Urhie.

An kama su da lodin ɗanyen mai cike da tankar jirgin ruwa a jihar Delta. Tankar jirgin ruwan dai ta na da lamba 7323473.

Mai Shari’a ya yi ƙorafin cewa tsatsauran hukunci ya kamata a yanke masu, saboda su na yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, kuma abin da su ka sata zai iya saisaitawa da sauƙaƙa wa ɗimbin ‘yan Najeriya ƙuncin rayuwa.

Abang ya ce ba haka ake yaƙi da cin rashawa da masu karya tattalin arzikin ƙasa ba.