Yadda jihohin da suke samun kaso mai tsoka daga Gwamnatin tarayya suka kasa saka yara makaranta a jihohin su

Sakamakon binciken da PREMIUM TIMES ta yi ya nuna cewa akwai jihohi 9 daga cikin jihohi 36 da Abuja da ke karbar kaso mai tsoka daga asusun gwamnatin tarayya kuma sune suka fi yawan yara dake gararamba a titiuna basu zuwa makaranta.

Jaridar ta gudanar da binciken ne jihohin 36 da Abuja daga shekaran 2015 zuwa 2018.

Bisa ga sakamakon binciken daga shekaran 2015 zuwa 2018 gwamnatin tarayya ta raba wa jihohin kasar nan banda Abuja Naira tiriyan 7.5.

Jihohin Kano, Akwa Ibom, Ondo, Borno, Katsina, Oyo, Jigawa, Niger da Kaduna na daga cikin jihohin da suka fi samun kaso mai tsoka amma jihohin ne kuma suka fi yawan yaran dake gararamba ba su zuwa makaranta.

Jihar Akwa-ibom daya daga cikin jihohin da ake hako man fetur a kasar nan kuma jihar da ta karbi mafi tsoka daga cikin kason har naira biliyan 606 ita ce jiha ta biyu a jerin jihohin da suka fi yawan yaran da basu makaranta.

Na biyu ita ce jihar Kano wacce ita ce jiha ta shida a jihohin da suka fi samun kaso mai yawa daga Abuja amma kuma yara ba su makaranta.

Sauran jerin jihohin dake samun kaso mai tsoka kuma ke da yawan yaran dake gararamba sun hada da jihar Ondo dake samun naira biliyan 199.3, Barno- Naira biliyan 185.2, Katsina- Naira biliyan 184.2, Oyo- biliyan 176.2, Jigawa-biliyan 174.6, Niger- biliyan 172.7 da Kaduna-biliyan 171.8.

Bisa ga rahoton yawan yaran dake gararamba a kasar nan da hukumar UBEC ta gabatar a shekarar 2018 ya nuna cewa jihar Kano na da yara 989,234 da basu makaranta.

Akwa-Ibom-581,800, Katsina-536,122, Kaduna-524,670, Oyo-418,900, Jigawa-337,861, Borno-330,389, Ondo-317,700 da Niger-292,700.

Bayan haka jihohin Delta dake karban Naira biliyan 541.8,Bayelsa- Naira biliyan 438.7,Edo- Naira biliyan180.4 na daga cikin jihohin da suka fi karancin yaran dake gararamba a titi.

Jihar Delta na da yara 145,996, Edo – 140,798 da Bayelsa – 53,079.

Yawan harajin da kowace jihar da Abuja ke samu a kasar

Jihohi 36 da Abuja sun Tara kudin harajin da ya kai naira tiriyan 11.1 a cikin shekara hudu.

Sai dai a cikin lissafin kudaden harajin da aka Tara din ban da kason jihar Ebonyi da Abuja ta shekaran 2015, Banda Totalkuma na Abuja ta shekaran 2016 da na 2017.

Daga cikin Naira tiriyan 11.1 din da aka tara jihar Legas ta tara Naira tiriyan 1.6, Rivers ta Tara Naira biliyan 865.5, Delta- biliyan 737, Akwa Ibom- biliyan 684.2, Bayelsa- biliyan 481.5, Ogun- biliyan 391.7 da Kano- biliyan 380.5.

Sauran jihohin sun hada da Edo- biliyan 276.4, Oyo- biliyan 257.8, Kaduna-biliyan 256.4, Ondo- biliyan 253.8, FCT-biliyan 233.4, Enugu- biliyan 229.8, Anambra-biliyan 225.7, Abia- biliyan 214.5.

Daga cikinsu dai jihohin Akwa Ibom, Kano, Oyo, Ondo da Kaduna ne suka fi tara kudaden haraji Kuma suka fi yawan yaran da basa makaranta a kasar nan.

A wani fannin kuma jihohin Delta, Bayelsa, Edo, Enugu, Anambra, Abia da Abuja sun yi kokari wajen rage yawan yaran da suke da su da basa makaranta.

Sannan a duk jihohin kasar nan da Abuja jihohin Legas da Ogun ne kadai basa jiran kudaden dake shigowa aljihusu daga asusun gwamnatin tarayya saboda kudaden harajin da suke tarawa na wadatar da su.

Yawan yaran da basa makaranta a Najeriya

Bisa ga rahoton da hukumar UBEC da NBS ta gabatar a shekarar 2018 ya nuna akwai yara sama da miliyan 10.2 da basa makaranta a kasar nan.

Lissafi ya nuna cewa kowace jihar daga cikin jihohin 10 din da yaran da basa makaranta ke zama akwai akalla yara miliyan 5.2 da basu taba zuwa makarantar firamare ba.

Rahoton ya kuma nuna cewa yara miliyan 10.2 din da basa makaranta sun fi kashi 60% na yara miliyan 40.8 masu shekara shida zuwa 11 da ke makarantar firamare.

Hakan ya nuna cewa a cikin yara hudu da suka isa zuwa makaranta daya baya zuwa makaranta a Najeriya.

Jihohin da ke karban karamin kaso daga asusun gwamnati Kuma ke da karancin yaran da basa makaranta.

Akwai jihohi 9 dake karban karamin kaso daga asusun gwamnati sannan suna da karancin yaran da basa makaranta a kasar nan.

A cikin shekara hudu jihar Osun ta karbi Naira biliyan 99.6 daga asusun gwamnati Amma yaran da basa makaranta a jihar sun Kai 165,114 a jihar.

Ita ma Ekiti ta karbi naira biliyan 120.2 sannan tana da Yara 50,945 da basu makaranta.

Jihar Cross Rivers ta karbi naira biliyan 122.2 a cikin shekara hudu kuma tana da yara 97,919 da basu makaranta.

Gombe ta karbi naira biliyan 132.9 amma yard 162,000 na gararamba a jihar.

Kwarai ta karbi naira biliyan 133 amma yara 84,247 basu makaranta a jihar.

Jihar Ebonyi ta karbi Naira biliyan 135.5 sannan tana da yara 145,373 da basa makaranta.

Nasarawa ta karbi naira biliyan 138.9 tana da yara 187,000 da basa makaranta.

Enugu ta karbi naira biliyan 153.3 sannan yara 82,050 basu makaranta.

Abia ta karbi Naira biliyan 158.7 da yara 91,548 da basu makaranta.