Yadda Gwamnoni Suka Sauya Matsaya Dangane Da ‘Yancin Cin Gashin Kai Ga Bangaren Ma’aikatan Majalisa Da Shari’a A Najeriya

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun sauya matsayarsu a kokarinsu na samo mafita mai dorewa kan yajin aikin gama-gari sakamakon fafutukar da kungiyar ma’aikatan kungiyoyin bangaren shari’a da majalisun jihohi na Najeriya ke yi na neman a aiwatar da ‘yancin cin gashin kansu.