Yadda Gwamnatin Buhari ke gaganiya da hoɓɓasar daƙile matsalar tsaro – Minista Aregbesola

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa an bada umarni da oda ga dukkanin ɓangarorin tsaron ƙasar nan cewa su kakkaɓe dukkan masu kawo ƙalubale ga tsaron Najeriya a faɗin ƙasar nan, a duk inda su ke.

Aregbesola ya ƙara jaddada wannan umarni da aka bayar a baya, inda ya ce kuma tun daga lokacin da aka bayar da umarnin, har yau ba a nuna alamar jan-ƙafa, ɓata lokaci ko sassautawa ba.

Aregbesola ya yi wannan bayani a ranar Alhamis. Amma kuma a cikin makon ne ‘yan bindiga su ka tare hanyar Abuja zuwa Kaduna, su ka shafe kwanaki huɗu a jere su na kwasar matafiya, su na garkuwa da su a cikin daji.

A rana ta farko sun kashe tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara, su ka kama dogarin ɗan sandan sa.

Yanzu haka ya na hannun ‘yan bindiga, kuma sun ce sai an biya su naira miliyan 200 za su sake shi.

Amma kuma yayin da Aregbesola ke amsa tambayoyin manema labarai, a ƙarshen Taron Majalisar Tsaron Ƙasa (NSC), a Fadar Shugaban Ƙasa, Aregbesola ya ce “a wannan lokacin za a ga gagarimin ci gaba sosai ”

“Matsawar muna raye ba za mu saurara ba, har sai mun cika burin mu na ganin an samu cikakken tsaro a Najeriya.”

“Saboda haka ina tabbatar da cewa wannan sabon umarni da aka ba sojoji, ‘yan sanda, jami’an leƙen asiri da sauran ɓangarorin jami’an tsaro, tabbas zai wanzar da zaman lafiya a cikin ƙasar nan.”

An tambaye shi wane ƙoƙari ake yi dangane da ƙoƙarin da ‘yan bindiga ke yi na ƙwace titin Abuja zuwa Kaduna?

Sai Aregbesola ya ce an ƙara jami’an tsaro, kuma an tura jami’an sintiri, masu shawagi da masu leƙen asirin gano maharan a kakkaɓe su.

Aregbesola ya yi wannan bayani kwana ɗaya kafin Babbar Kotun Tarayya ta ayyana ‘yan cewa ‘yan ta’adda ne.

Wannan jarida ta buga labarin cewa Kotu ta ayyana cewa masu garkuwa da ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne.

A labarin, Babbar Kotun Tarayya ta ayyana ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane cewa su ma ‘yan ta’adda ne, kamar Boko Haram da ISWAP.

Wadda hukunci ya ƙarfafa kiraye-kirayen da jama’a su ka riƙa yi wa gwamnatin tarayya cewa ta ɗauki ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram duk matsayi ɗaya, ‘yan ta’adda ne gaba ɗayan su.

Daraktan Gurfanar da Masu Laifi a Kotu na Tarayya (DPP) Mohammed Abubakar ne ya shigar da muradin neman kotu ta ayyana su matsayin ‘yan ta’adda.

An shafe shekaru 10 ‘yan bindiga na addabar wasu yankuna na Arewacin ƙasar nan. Har ta kai abin kusan ya zama bala’i a yankunan Arewa maso Yamma baki ɗaya.

Da ya ke gabatar da muradin, Abubakar ya shaida wa kotu cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun amincewa da ayyana ‘yan bindiga matsayin ‘yan ta’adda.

Da ya ke zartas da hukunci, Mai Shari’a Taiwo Taiwo, ya ce munanan ayyukan da ‘yan bindiga da masu garkuwa ke yi cewa ta’addanci ne ƙarara.

Takardun bayanan da ke gaban kotu sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga matsayin ‘yan ta’adda, saboda a na kashe mutane, garkuwa da mutane, banka wa garuruwan da ƙauyuka wuta da kuma yi wa mata da ‘yan mata fyaɗe.

“Gwamnatin Tarayya ta ƙara kafa hujja da yadda su ke garkuwa da ƙananan yara, musamman ɗaliban sakandare da na Islamiyya, satar shanu, bautar da mutane, ɗaure mutane, ƙuntata wa waɗanda su ka kama, tsare mata su na lalata da su tsawon lokaci, ɗirka wa matan mutane da ‘yan mata ciki, hare-hare da lalata kayan gona da sauran dukiyoyin jama’a.”