Yadda dan majalisan Najeriya ya kantara karya kan motoci yakin da kaar china ta baiwa Najeriya – Binciken DUBAWA

Zargi: A wani labarin da aka wallafa a Facebook, a shafin wani mai suna Joe Igbokwe, jigo a jam’iyyar APC kuma mai baiwa gwamnan Legas shawara, ya yi zargin wai kasar China ta baiwa rundunar sojojin Najeriya sabbin motoci masu sulke guda 100.

Labarin wanda mutane da dama suka karanta gani ya fito a shafin Joe Igbokwe jigo a jam’iyyar APC kuma mai bai gwamnan Legas shawara a ofishin kula da magudanar ruwa ranar talata 9 ga watna Nuwamba, inda ya yi bayani kamar haka, “China ta baiwa rundunar sojojin Najeriya motoci masu sulke guda 100. Da fatan Najeriya za ta yi nasara.”

Tantancewa

Shin kasar China ta kawo motoci masu sulke Najeriya?

An aika wa Igbokwe sakon tes da e-mail don tantance kalaman na sa. Bayan nan kuma an tuntube shi ta wayar tarho. Da aka yi mi shi tambayar inda ya sami labarin da ma gaskiyar shi, bai amsa ba.

Ce wa ya yi: “Ku je ku bincika”

To sai dai rahotanni daga kafafen yada labarai musamman daga 28 ga watan Oktoba 2021 sun bada tabbacin cewa rundunar sojin Najeriya ta karbi motoci masu sulke guda 60 daga kasar China, wadanda za su taimaka a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram da kuma ‘yan bindiga a yankunan Arewa maso gabas da Arewa maso yammacin kasar.

Baya ga haka, rahotannin sun kuma kara da cewa rundunar sojojin har ta kaddamar da wadannan motocin domin shawo kan kalubalen rashin tsaron da take fiskanta. Rahotannin sun ce an kaddamar da motocin a makarantar sojojin kasa da ke Jaji a jihar Kaduna a karkashin jagorancin Manjo Janar Victor Ezugwu wanda ya wakilci shugaban hafsan sojoji Lt Gen Faruk Yahaya.

Haka nan kuma a wani bidiyon YouTube, gidan talbijin na Channels shi ma ya bayyana cewa rundunar sojojin ta kaddamar da motoci 60. Ranar 29 ga watan Oktoba 2021. Ko a rahotannin da aka yi a sauran kafafen yada labarai da manyan tashoshin talbijin da ke watsa labarai a Najeriya duk sun ce motoci 60 aka bayar.

A waje guda kuma, wata tashar labarai mai suna Defence Web ta buga labarin cewa rundunar sojin Najeriya ta sami wasu karin motoci 100.

A karshe

Duk kafofin yada labarai masu nagarta a kasar sun ce motoci 60 China ta bayar dan haka maganan Joe Igbokwe ba gaskiya ba ne kuma hakan na iya ruda jama’a