Yadda dakarun Najeriya suka kashe Boko Haram 29, suka ceto mutum 52 da suka yi garkuwa da su

Sojin Najeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe Boko Haram/ ISWAP 29 sun kuma kama 55 cikin su. Bayan haka sun ceto mutum 52 da aka yi garkuwa da su duk a tsakanin makonni biyu da suka gabata.
Darektan yada labarai na Hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya, manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka ranar Alhamis da yake bayani kan nasarorin da sojojin Najeriya suka samu a cigaba da arangama da suke yi da Boko Haram yankin Arrwa Maso Gabas.
Onyeuko ya ce ‘yan Boko Haram 1,755 sun tuba inda a cikinsu akwai maza 280, mata 523 da yara kanana 952.
Bayan haka ya kara da cewa sojoji sun yi arangama da wasu ƴan bindiga a hanyar Uzoro zuwa Gadamayo dake jihar Adamawa inda suka kashe mutum daya sauran sun gudu sun bar makaman su.
Onyeuko ya ce a ranar 6 ga Agusta dakarun tare da hadin gwiwar CJTF sun kama mutum uku dake kawo wa mahara kaya da suka hada da Hussain Dungus, Ali Bulama Jidda and Malam Ali Abuna duk a kauyen Buni Yadi jihar Yobe.
A ranar 3 ga Agusta sojojin saman Najeriya sun kashe kwamandan Boko Haram Alhaji Modu wanda aka fi sani da ‘Bem Bem’ da wasu abokan sa ta hanyar yi musu luguden wuta daga sama.
“Mazauna yankin sun ce an kashe mahara 20 yayin da suke wani taro kitsa makirci.
“Sojoji sun kama harsasai 128 Kiran 7.62mm, kekuna biyar, bindiga kirar AK-47 guda 12, babura 4 da wayoyin hannu 5.