Yadda a baya muke tunanin cewa cutar Nimoniya cutar aljanu ce – Wasu mata a Jigawa

Wasu mata a Karamar Hukumar Kiyawa dake Jihar Jigawa sun fahimce cutar sanyi ta Nimoniya ba cutar aljanu bace kamar yadda suke tunanin hakan a can baya.

Sun bayyanawa Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA hakan a wajen taron Ranar yaki da cutar Nimoniya ta Duniya wanda aka yi fadar hakimin Kiyawa kuma Dan Masanin Dutse, Adamu Aliyu.

Taron wanda hukuma mai zaman kanta ta “Save the Children International” ta dauki nauyi, ya tattaro Mata daga garuruwa da unguwaninni na Karamar Hukumar Kiyawa domin duba nasarori da aka samu wajen wayar da kai akan cutar sanyi ta Nimoniya mai kashe Yara kanana.

Fatima Muhammad, wata jami’ar sa-kai, kuma uwa, ta ce ana ci gaba da wayar da kan mata mazauna karkara kan yadda za su kare ‘ya’yansu daga kamuwa da cutar ta Nimoniya da kuma yadda za su gano wanda ya kamu da ita.

Ta ce a baya sun dinga tunanin cewa Nimoniya cutar aljanu ce saboda sun ga yadda yara su ke shan wahala a wajen numfashi da kuma yadda su ke suma idan suna fama da cutar.

Ta ce amma bayan ‘Save the Children International’ ta wayar musu da kai ta kafafen watsa labarai sai suka yi watsi da wancan tunanin nasu kuma suna zuwa asibiti domin duba lafiyar iyalansu.

Malama Fatima ta kuma cewa, shiga dakin girki da Yara kanana suna shakar hayaki daga icen garki babban illace ga lafiyar yaransu.

A halin yanzu mun kuma gano cewa cutar sanyi ta Nimoniya tana da alaka da shakar gurbataccen iska da mahalli mara tsafta, inji malama Fatima.

Ita ma Amina Awaisu, mamba a Ƙungiyar Mata Musulmai, ta ce mata da yawa ba su san da Nimoniya ba, amma sakamakon ci gaba da wayar da kan jama’a an samu canji.

Amina ta ce an samu raguwar mutuwar Yara kanana a Karamar Hukumar Kiyawa ne sakamakon wayar da kan jama’a, Kan yadda cutar sanyi ta Nimoniya take kama Yara.

Ta ce a baya yara da yawa sun mutu a gida ba tare da an sani ba saboda iyayensu sun ki kai su asibiti, suna cewa cutar aljanu ce.

HANYOYIN YAƊUWAR CUTAR NIMONIYA

Masana cutar ta Nimoniya a wajen taron sun bayyana nau’ikan ƙwayoyin cututtukan da ke haddasata.

Cutar ta Nimoniya tana faruwa ne sakamakon kamuwa da ƙwayoyin cututtuka na bakteriya ko bairos (masu haddasa mura/ mashasshara).

Mai faruwa sanadiyyar ƙwayoyin bakteriya tana yaɗuwa daga mutum zuwa mutum ta hanyar shaƙar majina/kaki da masu cutar kan fitar yayin magana ko tari.

Amma ita mai faruwa sakamakon kamuwa da fungai bata yaduwa daga mutum zuwa mutum saidai ana daukarta ne daga muhalli mara tsafta.

Abin da ya sa ake samun yawaitar Nimoniya a Kiyawa -Jami’i

Jami’an lafiya a Jihar Jigawa sun ce ana ci gaba da samun ƙaruwar yara masu kamuwa da cutar sanyi ta Nimoniya a watanni uku na tsakiyar 2021 a ƙaramar hukumar Kiyawa.

Muhammad Kani, Manajan Cibiyar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Kiyawa ya bayyana hakan ne a yayin taron ‘Ranar yaki da Cutar Nimoniya ta Duniya a Kiyawa’.

Malam Kani ya shaida wa manema labarai cewa a baya ba a san adadin yara da suke fama da cutar sanyi ta Nimoniya ba saboda jami’an lafiya ba su da ƙwarewar gano cutar.

Ya ce a watanni uku na farkon wannan shekara, an samu karuwar mace macen Yara kanana wanda ya kai kaso 12.6 cikin ɗari.

Amma Ya ce a watanni uku na tsakiyar wannan shekara, an samu raguwar mutuwar Yara a Karamar Hukumar Kiyawa da kaso 3.9 cikin ɗari saboda ana samun cigaba da gano cutar Nimoniya a Yara kanana kuma ana basu magani suna warkewa.

Kani ya ce ƙaramar hukumar Kiyawa wadda take a Jigawa ta Tsakiya ita ce ta fi kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 27 na jihar yawan masu ɗauke da Nimoniya.