Yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 16 suka yi garkuwa da mutane da dama a jihar Taraba

Akalla mutum 16 ne ƴan bindiga suka kashe sannan suka yi garkuwa da wasu mutane da dama a ƙauyukan jihar Taraba ranar Juma’ar makon jiya.
Jaridar Daily Post wanda ta wallafa labarin ya ce maharan sun afka kauyen a safiyar Asabar bisa babura.
Kauyukan da maharan suka shiga sun hada da Garinkuka da Gidado dake karamar hukumar Gassol.
Wani ma’aikacin karamar hukumar Abdullahi Chul ya ce maharan sun shigo kauyukan suna ta harbi ta ko Ina inda a dalilin haka mutane da dama suka ji rauni a jikinsu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Usman ya tabbatar da aukuwar wannan hari yana mai cewa tuni rundunar ta fara gudanar da bincike da kuma bibiyan ƴan bindigan.
Idan ba a manta ba a kwanakin bayan ‘yan bindiga sun tare matafiya a hanyar zuwa karamar hukumar Gassol inda suka kashe direban tirela sannan suka yi garkuwa da matafiya da dama a hanyar.
Mahara sun kashe mutum 13 a kauyen Karekuka dake karamar hukumar.
‘Yan bindigan sun afka kauyen ranar Juma’a suka yi arangama da ‘yan sa kan kauyen.
Akalla ‘yan sa kai 7 da ‘yan bindiga 6 suka mutu a sanadiyar wannan batakashi da suka yi baya fa mutane da dama da suka riga mu gidan gaskiya a dalilin wannan arangama.