Yadda Ɗa ya rika ɗirkawa mahaifiyar sa ciki har sau uku a jihar Kwara

Rundunar tsaro na Sibul Defens a jihar Kwara NSCDC ta kama wani matashin saurayi da ya rika dirka wa mahaifiyarsa ciki har sau uku a jihar a jihar Kwara.
Kakakin rundunar Babawale Zaid Afolabi ya ce Adamu da mahaifiyarsa Fati Sime sun haifi ‘ya’ya uku tare.
“A ranar 09 ga Satumba 2021 dagacen kauyen Moshe dake karamar hukumar Kaiama Malam Bandele ya kawo kara a ofishin jami’an tsaro cewa an kama Adamu Sabi Sime da mahaifiyarsa Fati Sime suna lalata kuma har sun haifi ‘ya’ya uku tare.
” Daya daga cikin ‘ya’yan Fati ya tabbatar wa jami’an tsaro abinda ya auku tsakanin babban dan da mahaifiyar su.
Babawale ya ce sakamakon binciken da jami’an tsaro suka gudanar ya nuna cewa Adamu da Fati ‘yan kasar Benin ne Kuma sun shigo Najeriya ba tare da izini ba.
Ya ce rundunar NSDCD ta damka Adamu da Fati ga hukumar NIS domin ci gaba da gudanar da bincike akai.