WUYA KO DA MAGANI BA DAƊI: IPOB sun soke tilasta zaman gida, sun goyi bayan fitowa zaɓen gwamnan Anambra

Haramtacciyar ƙungiyar IPOB ta soke tilasta zaman gida tilas da ta ƙaƙaba a Jihar Anambra.

Kungiyar wacce aka sani da zafi wajen ƙaƙaba dokar tilasta zaman gida a yankin Kudu maso Gabas, a baya ta ce ba za ta bari jama’a su fita su kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan Anambra, ranar Asabar mai zuwa ba, wato ranar 6 Ga Nuwamba.

IPOB ta yi sanarwar cewa daga ranar Juma’a 5 Ga Nuwamba za su hana kowa fita a jihar Anambra.

IPOB Ta Saduda: Sai dai kuma wata sanarwa da Kakakin IPOB mai suna Emma Powerful ya fitar da yammacin yau Alhamis, ta na ɗauke da bayanin cewa IPOB ta janye dokar hana jama’a fita ɗin.

“Saboda dattawan mu sun shigo cikin lamarin, su da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, kuma mun fahimci sun shigo ne domin sun fahimci inda muka dosa.

“Saboda haka shugabannin IPOB a ƙarƙashin Nnamdi Kanu sun janye dokar tilasta wa jama’a zaman dirshan a gida, wacce aka tsara cewa za ta fara aiki daga gobe Juma’a, 5 Ga Nuwamba zuwa 10 Ga Nuwamba, 2021.”

Yanzu dai IPOB ta amince kowa ya fito ya jefa ƙuri’a a ranar Asabar, a zaɓen Gwamnan Jihar Anambra.

Sai dai kuma IPOB ba ta nuna goyon bayan kowace jam’iyya ɗaya ba, daga cikin jam’iyyu 18 da suka tsaida ɗan takarar gwamna a zaɓen.

Idan ba a manta ba, a ranar Talata yayin da su ke mahawara, ‘yan takarar gwamnan jihar Anambra fitattu su bakwai duk sun ce idan su ka hau mulkin jihar Anambra, za su zauna teburin sasantawa da IPOB.

Tuni dai takara ta yi zafi sosai tsakanin ‘yan takarar APC, APGA da PDP.