WUJI-WUJI INA GABAS: Ni kaina ban gane hanyar gida na ba, yadda El-Rufai ya canja fasalin jihar da suntuma-suntuman ayyuka – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a jihar Kaduna ranar Alhamis.

Shugaba Buhari da dira Kaduna ranar Laraba da dare ya kaddamar da wasu gaggan ayyuka wanda gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya yi a faɗin jihar.

Da ya ke kaddamar da katafaren dandalin Murtala Square wanda gwamnatin El-Rufai ta maida ita sabuwa, shugaba Buhari ya ce abinda El-Rufai ya yi a Kaduna ba a taɓa yin irin sa ba.

” Wuji-wuji ina gabas, abinda ake yi wa yara, a jujjuya su sai a ajiye yaro a ce masa ina gabas, sai ya yi ta juyejuye yana neman gabas. Haka kayi wa jihar Kaduna.

” Ni kai na da kyar zan gane inda hanyar gudanar da na yake, saboda yadda ka inganta fasalin jihar da maida shi abin alfahari ga kowa

Baya ga Murtala Square, Buhari zai kaddamar da babbar gadar Kawo, da wasu manyan tituna wanda aka maida su zuwa da dawowa.

Bayan cikin garin Kaduna, Buharizai kaddamar da ayyuka a Kafanchan. Daga nan kuma sai gaba ɗaya a ɗunguma zuwa Zaria ranar Juma’a domin kaddamar da wasu ayyukan ci gaba da gwamnatin El-Rufai ta yi a tsawon shekaru 7 na mulkinsa.

Tabbas, ga duk wanda ya san Kaduna kafin zuwan gwamnatin El-Rufai, ya san cewa lallai an yi abin da ba a taba yi a jihar ba tun bayan ayyukan da sardauna Gamji ya yi a baya.