Wole Soyinka ya yi tir da bidiyon barkwanci da shegantakar ‘yan ƙungiyar ‘Pyrates Confraternity’ kan Tinubu

Wole Soyinka ya nuna rashin jin daɗin yadda wasu mambobin ‘Pyrates Confraternity’ su ka watsa wani bidiyo inda su ke nuna alamun cin fuska ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu.
An nuno su a cikin jerin gwano su na rera waƙa mai aibata Tinubu, wadda a yanzu haka ta game duniya. Lamarin da Soyinka ya ce yin hakan rashin mutunci ne, kuma abin ƙyama ƙwarai.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Soyinka ya ce a gaskiya hankalin sa ya kaɗu sosai kuma zuciyar sa ta dugunzuma da ya ji wakar.
“Ni na tashi a cikin al’adar da ba a yarda ana maida wani naƙasu ko tawayar mutum abin dariya ba ko a riƙa yi masa shegantaka. Kuma addinin Yarabawa ma ya yi hani da yin irin wannan shegantaka. Duk irin abin da mutum ya same shi, bai dace a riƙa yi masa shegantaka har ya zama abin dariya ko abin aibatawa ba.
“A haka mu ka tashi a cikin wannan tarbiyya ta mutunta ɗan Adam komai irin nakasun da ya ke da shi. Domin babu wanda ya fi ƙarfin samun tawaya.”
A cikin bidiyon, Kungiyar ‘Pyrates Confraternity’ na bikin cikar ƙungiyar shekaru 70 da kafuwa, su na sanye da rigunan su na ƙungiyar asiri mai launin fari da ja, su na rera waƙa kan Tinubu, yayin da hannayen su da ƙafa ke karkarwa, kamar yadda Tinubu ke yi. An nuno Tinubu ɗin hannun sa na rawa, ya na cewa, “wannan ne lokacin da zan zama shugaban ƙasa.”
Waƙar dai shegantaka ce ta Tinubu tun bayan kakkausan kalaman da ya yi a Gidan Gwamnatin Ogun kafin a yi zaɓen fidda gwani.
Tuni dai ake ta yaɗa bidiyo iri daban-daban inda ake kwaikwayon Tinubu cikin barkwanci da shegantaka, musamman a ko’ina cikin faɗin ƙasar nan.