WATA SABUWAR RIGIMA: Malaman jami’o’i sun ci kwalar Hukumar NITDA sun kira hukumar da shugaban ta maƙaryata

Yayin da Gwamnatin Tarayya ta zuba ido harkokin ilmin jami’a ya shiga garari, a na su ɓangaren, Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta tofa wa Hukumar Inganta Fashar Zamani (NITDA) miyau tare da kiran hukumar da shugaban ta maƙaryata.

Shugaban ASUU na Ƙasa Emmanuel Osodeke ya yi tir da Shugaban Hukumar NITDA, Kashifu Inuwa tare da kiran sa maƙaryaci, biyo bayan furucin da Inuwa ya yi a kan tsarin biyan albashin malaman jami’o’i na UTAS, wanda ASUU ke so a fara biyan su albashi da shi, ba tsarin IPPS na gwamnatin tarayya ba.

Tsarin na UTAS dai a yanzu haka ana ci gaba da jaraba shi da auna nagarta, inganci da sahihancin sa, kafin a fara amfani da shi.

Hukumar NITDA da haɗin guiwar ASUU ke yin jarabawar gwajin.

To sai dai kuma kwanan nan Shugaban NITDA Kashifu Inuwa ya faɗa wa manema labarai cewa tsarin biyan albashi na UTAS da ASUU ke so a ƙirƙiro ya kasa haye siraɗin jawabawar matakai uku da aka yi masa. Haka Inuwa ya bayyana wa manema labarai ca Fadar Shugaban Ƙasa.

Shi kuma Shugaban ASUU ya ƙaryata Shugaban NTDIA, inda ya ce a cikin jarabawar da aka yi, har ma akwai inda UTAS ya ci maku 85.

“Don haka mu na jan hankalin Shugaban NTDIA Kashifu Inuwa cewa ya kame bakin sa ya yi shiru, tunda ba a kammala gwajin ba tukunna.

“Idan kuma bai daina ba, to za mu tilasta wa NTDIA ta fito da sakamakon gwajin da UTAS ya samu maki 85 domin kowa ya gani kuma ya tabbatar.

Kafin fitar da bayanin bayan taro, wakilin mu ya ruwaito cewa ASUU ta ƙara maƙonni 8 kafin ta sake waiwayen Gwamnatin Tarayya, ta ce ‘gwamnatin maƙaryata’ ce.

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta bayyana ci gaba da yajin aiki har ƙarin tsawon watanni biyu nan gaba, kafin ta sake waiwayar Gwamnatin Tarayya.

Shugabannin ASUU sun kwana taro a Hedikwatar su da ke Jami’ar Abuja, wanda su ka fara tun daga ranar Lahadi, har zuwa wayewar garin yau Litinin.

Wata majiya daga cikin mahalarta taron ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa tabbas sun kwana taro, kuma sun yanke shawarar cewa za su ci gaba da yajin aiki, tunda gwamnatin tarayya ta ɗauke su sakarkaru.

Majiyar wadda ta ce kada a ambaci sunan ta, ta ce za su ci gaba da jayin aiki har sai sun nuna wa gwamnatin tarayya cewa lallai ta watsar da ilmi a ƙasar nan, ta bar shi ya na neman lalacewa.

Majiyar ta ce yanzu haka ana nan ana rubuta takardar bayan taro wadda za a raba wa manema labarai.

Malaman inji majiyar sun zargi Gwamnatin Tarayya da rashin cika alƙawari, yin baki biyu da kuma zumbuɗa ƙarya.

A baya dai bayan gwamnati ta sha yi wa ASUU alƙawari, kwanan baya Gwamnatin Tarayya ta fito ta ce ba ta da kuɗaɗen da za ta iya biyan buƙatun malaman jami’o’i.

Dama kuma watanni biyu baya ASUU ta ce idan sun sake tafiya yajin aiki, to a tuhumi Buhari, gwamantin sa ce ta kasa cika masu alƙawari ko da guda ɗaya.