Wabba ya ja zugar ‘Yan kungiyar Kwadago zuwa gidan gwamnatin Kaduna

Duk da cewa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa gwambati na neman shugaban NLC Ayuba Wabba ruwa a jallo, kwatsam ku sai ga shi da dandazon yan kungiyar Kwadago sun dunguma zuwa gidan gwamnatin jihar Kaduna.

NLC ta ce za ta yi zanga-zanga har na kwana biyar a jihar Kaduna wa da hakan ya sa kusan komai ya tsaya cak a jihar.

Babu ruwa babu wuta ba, nan fetur, komai ya tsaya cak a jihar.

Gwamnan jihar Kaduna ya Nasir El-Rufai ya yi kira ha ‘Yan Kaduna su nemo masa shugaban kungiyar Kwadago Ayuba Wabba, cewa wai shi mai laifi ne.

El-Rufai ya rubuta a shafin sa ta tiwita cewa duk wanda ya fadi wa gwamnati inda Wabba ke boye za a bashi ladar kudi masu yawa.

Ya ce yajin aikin da Wabba ya kira a jihar Kaduna, ya saba wa doka, saboda haka gwamnati na neman sa a cafke shi, kuma duk wanda ya bada bayanan inda yake ko ya yi sanadiyyar aka kama shi za a bashi kyautar kudi mai tsoka.

Yau an shiga cikin kwana na uku a yajin aikin da ake yi a jihar Kaduna.

Sai dai kuma an samu rahoton, cewa wasu matasa sun afka wa masu zanga-zanga a daidai shataletalen Kamfani NEPA a Kaduna.