Wa’adin watanni uku da CBN ya bayar na canja tsoffin takardun kudi ya min daidai- Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadin ya ce matakin da babban bankin Najeriya CBN ya dauka na sauya wasu takardun manyan kudi ya samu goyon bayansa kuma yana da yakinin cewa al’umma za su ga alfanun hakan.

Ya bayyana hakan ne a hirar da gidan Talabijin na Tambarin Hausa tare da fitattun ‘yan jaridan nan Halilu Ahmed Getso, da Kamaluddeen Sani Shawai wanda zai zo a safiyar Laraba mai zuwa, a cewar wata sanarwa da Kakakin Shugaban Garba Shehu ya fitar.

Shugaba Buhari ya ce dalilan da CBN ya ba shi sun tabbatar masa da cewa tattalin arzikin kasar nan zai farfado ta hanyar faduwar raguwa hauhawar farashin kaya, jabun kudin da kuma yawan kuɗaɗen da ke yawo.

Ya kuma ce bai ganin wa’adin watanni uku na canjin tsoffin takardun kudin da sabbin da CBN ya bayar a matsayin ya yi kadan.

“Mutanen da ke da haramtattun kudaden binne a karkashin kasa za su fuskanci kalubale da wannan tsari amma ma’aikata, ‘yan kasuwa da ke da halastattun hanyoyin samun kudaden shiga ba za su fuskanci matsala ba.”

A cikin hirar, shugaban ya kuma yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi samar da abinci da tsaron kasa da dai sauransu.