TUNATARWAR ATIKU GA ‘YAN JIHAR NEJA: Ku tuna da ibtila’in da mulkin APC ya jefa ku ciki

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga jama’ar Jihar Neja da sauran ‘yan Nijeriya da su tuno da shekaru sha shida na mulkin PDP kuma su kwatanta su da shekaru bakwai na mulkin gwamnatin APC da ya kawo matsanancin baƙin ciki da wahala da fatara da yunwa da bala’i da rashin tsaro ga al’umma.
Daga nan ya yi kira ga ‘ya’yan jihar da ma ‘yan Najeriya baki ɗaya da su tabbatar sun aje kyakkyawan tarihi da kyautata wa ‘yan baya ta hanyar korar gwamnatin APC ta hanyar ƙin zaɓen dukkan ‘yan takarar ta a zaɓuɓɓukan da za a yi a watan gobe.
Atiku ya yi wannan kalamin ne a wajen taron yaƙin neman zaɓen PDP da aka yi a Minna, babban birnin Jihar Neja, a ranar Asabar.
Akwai alamun cewa filin Kasuwar Bajekoli da ke unguwar Shango a garin Minna bai taɓa ganin dandazon mutane ba irin wanda ya gani a ranar Asabar wajen karɓar baƙuncin Atiku da Gwamna Arthur Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.
Rundunar yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa ta isa Minna ne a ranar Asabar inda jama’a su ka yi dafifi domin tarbar su ta yadda filin ya cika ba masaka tsinke.
Tun misalin ƙarfe 8 na safe magoya bayan jam’iyyar su ka cika filin Kasuwar Bajekolin, a yayin da wasu kuma su ka nufi babban filin jirgin sama na Minna mai nisan kimanin kilomita daga cikin gari domin tarbar Atiku da Okowa, da kuma sauran manyan baƙi da su ka haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto, Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom, da tsofaffin gwamnoni Boni Haruna na Adamawa, Liyel Imoke na Kuros Riba, Malam Ibrahim Shekarau na Kano, da sauran su da dama.
Filin Kasuwar Bajekolin da ke Shango ya cika maƙil da dubban magoya bayan jam’iyyar PDP. Wasu ma daga wajen filin su ka tsaya, wanda hakan ya jawo cinkoson motoci cika a kan manyan hanyoyin Minna.
Tsohon gwamnan Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu (Talban Minna), wanda shi ne shugaban rundunar yaƙin neman zaɓen PDP a jihar a zaɓen 2023, shi ma ya yi kira ga jama’a da su fitar da APC daga mulkin jihar domin, a cewar sa, ba ta tsinana komai ba sai jawo baƙin ciki da wahala ga jama’a.
Sauran waɗanda su ka yi jawabi a taron sun haɗa da mataimakin Atiku a takara, wato Gwamna Okowa, da Shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, da Gwamna Aminu Tambuwal, da Dino Melaye, da Gimbiya Rakiya Atiku (maiɗakin Atiku Abubakar) da Sanata Zaynab Kure, da shugaban PDP na Neja, Tanko Beji, da Gwamna Emmanuel Udom na Akwa Ibom, da sauran su, waɗanda kowannen su ya shawarci masu zaɓe a jihar da su fitar da APC daga mulkin jihar da ma tarayya.
An ƙawata taron da hawan raƙuma da dawakai da raye-rayen gargajiya da waƙoƙin mawaƙa irin su Naziru Sarkin Waƙa da sauran su.
A ƙarshe, Dakta Babangida Aliyu ya shirya wa Atiku da sauran jiga-jigan jam’iyya walimar cin abincin rana a gidan sa.