Tun yanzu zan fara kwarara wa marayun Kaduna lagwada kafin in zama gwamna – Uba Sani

Sanata Uba Sani, ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na APC ya yi wa matan da ke da marayu karkashin su a jihar alkawarin cewa tun yanzu zai fara kwarara wa marayun lagwada daga aljihun sa kafin ya zama gwamnan Kaduna.
Uba wanda ya yi jawabi a wurin taron dubban mata na yankin karamar hukumar Igabi ya ce ” Ina matukar mika godiya ta ga matayen wannan yanki bisa soyayyan da suka nuna min karara da kuma karamci sannan kuma ina so in tabbatar wa mata duka na jihar Kaduna cewa za su shaida idan muka ɗare kujeran gwamnati.
Uba ya ce gwamnatin sa zata baiwa mata fifiko matuka sannan kuma da kula a koda yaushe. Ya ce za a saka su a cikin gwamnati domin a dama da su sannan kuma da basu dama domin cigaban su a jihar.
Za mu kara yawan mata a cikin geamnatin mu sannan kuma za mu fidda tsare-tsare da zai taimaka musu domin su samu taimako a harkokin sana’o’in su da kuma kasuwanci gaba ɗaya.
Wata wacce ta halarci taron ta zanta da wakilin mu a Kaduna bayan taron, ta mika godiyarta a madadin matan Igabi da na jihar Kaduna ga Sanatan sannan kuma da tabbatar da cewa lallai Uba Sani ne za su zaɓa kaf din su a yankin a lokacin zaɓe.