TSARO: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a cikin makonni biyu a Najeriya

‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a cikin makonni biyu daga ranar 28 ga Agusta zuwa 10 ga Satumba 2022.
Daga cikin mutanen da maharan suka kashe akwai jami’an tsaro biyar da mutanen gari biyar.
‘Yan sanda uku da sojoji biyu na daga cikin jami’an tsaron da ‘yan bindiga suka kashe a kasar nan.
Hakan ya nuna cewa kasar ta samu ragowa a yawan kisar mutanen da ‘yan bindiga ke yi.
Jihar Legas
Shugaban kungiyar masu motocin haya na jihar Legas ya gamu da ajalinsa a rikicin ‘yan kungiyar asiri da ya ritsa da shi a hanyar Mile 12 a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benjamin Hundeyin ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sakamakon binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa sunan mutumin Alhaji Sule.
Katsina
Sojoji biyu sun mutu sannan wasu mutum hudu sun ji rauni a harin da ‘yan bindiga suka kai wa sojojin bataliya ta 20 ranar 31 ga Agusta a jihar Katsina.
Mazaunan Shimfida inda sojojin suka yi batakashi da ‘yan bindigan sun ce sojin sun kashe ‘yan bindiga da dama a harin.
Jihar Borno
Boko Haram sun kashe mutum hudu inda a ciki akwai babban limamin Gima dake kauyen Ngulde karamar hukumar Askira-Uba ranar 4 ga Satumba.
Mutane da dama a kauyen sun ji rauni a jikinsu a dalilin harin.
Jihar Enugu
‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda uku a New Haven dake karamar hukumar Enugu ta Arewa.
Maharan sun kashe jami’an tsaron da misalin karfe 10:15 na dare.