Tinubu ya gana da Shekaru a Legas

A ranar Lahadi ce dai Jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya yi wa Sanata Ibrahim Shekarau gayyatar gaggawa zuwa Legas daga Abuja.

Makusantan Shekarau sun tabbatar da cewa jirgi sukutum Jagaban ya tura Abuja aka ɗauki Sanata Shekarau zuwa Legas, inda ya shafe sa’o’i uku su na ganawa.

Hadiman na Shekarau sun ce daga cikin batutuwan da aka tattauna, har da sarambe da azargagin da Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya yi a wurin zaɓen shugabannin APC, wanda ya janyo har jam’iyyar ta dare biyu a Kano.

An kuma tattauna yadda su ka shigar da ƙara da yadda kotu ta halsata zaɓen da ɓangaren Shekarau su ka yi, inda su ka zaɓi Haruna Ɗanzago a matsayin shugaban jam’iyya a Kano.

Sannan kuma Shekarau ya yi masa bayanin yadda aka banka wa ofishin su wuta, kwana biyu bayan da kotu ta ba su nasara da kuma yadda gwamnatin Kano ta rufe ofishin lauyan ɓangaren Shekarau.

Idan ba a manta ba, Prmii Times Hausa ta buga labarin cewa ɓangaren Shekarau da Sanata Barau Jibrin sun kai koke wurin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya.

Shekarau, Barau Jibrin da Sha’aban Sharaɗa sun aika wa Sufeto Janar da ƙorafi, sun zargi Abdullahi Abbas da laifin cinna wuta.

Tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Barau Jibrin da kuma Sha’aban Sharaɗa, sun rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Alƙali Usman wasiƙa mai ɗauke da ƙorafin banka wa Ofishin APC na Sanata Barau Jibrin wuta da wasu ‘yan daba su ka yi.

Wasiƙar wadda aka rubuta a ranar 2 Ga Disamba, ta na ɗauke har da sa hannun sauran Ɗan Majalisar Tarayya Nasiru Abduwa da kuma Tijjani Joɓe da Haruna Dederi.

Su shida duk sun danganta kai wa ofishin jam’iyyar da hukuncin da Kotun Tarayya ta bayar a Abuja, inda ta rushe tare da haramta zaɓen shugabannin jam’iyya na ɓangaren Ganduje, wanda aka ce shugaban jam’iyyar da ke kai, Abdullahi Abbas ne ya lashe.

Kotu ta haramta zaɓen su Abdullahi Abbas, daga jihar har zuwa matakin ƙananan hukumomi.

Kuna ta gargaɗe su cewa kada su kuskura su sake zaɓen shugabannin. Domin kotun ta amince da shugabancin ɓangaren su Shekarau, waɗanda su ka zaɓi Haruna Ɗanzago.

Premium Times ta bada labarin banka wa ofishin wuta kuma ta buga labarin yadda ‘yan sanda su ka kama mutum 13 da ake zargi na da hannu.

Takardar Ƙorafi Ga Sufeto Janar:

A cikin wasiƙar ƙorafin, su Shekarau sun zargi Abdullahi Abbas da alhakin ɗaukar nauyin waɗanda su ka banka wutar.

Cikin waɗanda aka zarga kuma har har da Kwamishinan Lura da Ƙananan Hukumomi, Murtala Garo, Faizu Alfindiki, wanda shi ne Shugaban Ƙaramar Hukumar da ya jagoranci rusa wani ginin koya wa matasa sana’o’i da Sha’aban Sharaɗa ya fara yi.

Sai kuma Khalid Diso Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, Hassan Garban Ƙauye na Ƙaramar Hukumar Kumbotso, sai kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Nasarawa.

Yayin da su ka yi kira ga Sufeto Janar da ya ɗauki matakin binciken gaggawa, sun kuma yi gargaɗin cewa idan wani abu ya same su ko magoya bayan su, to waɗannan da su ka ambata ne ke da hannu.

Sai dai kuma kakaki waɗanda aka zarga ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sharri ne aka yi masu.

Ahmed Aruwa ya ce su ma tashi su ka yi da safe su ka ji labarin an banka wutar. “Amma ba waɗanda aka lissafa cikin zargin ba ne su ka ɗauki nauyin ‘yan dabar.” Inji Aruwa.

Gayyatar Tinubu Ga Shekarau: Masu sharhin siyasa na ganin ɓarakar da ta kunno kai a cikin APC a jihar Kano, babbar baraka ce da za ta iya hana jam’iyyar yin nasara a Najeriya ɗungurugum, ba ma a Kano kaɗai ba.

Kowa ya san rawar da ɓangaren Shekarau ya taka wajen nasarar Ganduje a zaɓen 2019. Manyan jiga-jigan gwamnatin Ganduje da dama har da Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna, duk ‘yan gidan siyasar Shekarau ne.

Yayin da wasu ke ganin wataƙila Shugaba Muhammadu Buhari ne ya umarci Tinubu ya sasanta ɓangarorin biyu, wasu kuma na ganin Tinubu ne da kan sa ya shirya gayyatar, domin ya gyara miyar taushen tuwon takarar sa a zaɓen 2023, saboda ganin cewa duk wanda ya shiga farautar zaɓe da gurgun kare daga Kano, to kuwa ko ɓera ba zai iya kamowa ba.

Ko ma dai ya lamarin zai kasance, zai yi wahala ɓangarorin biyu su shirya, muddin dai Ganduje ya shigar da ɗaukaka ƙara a kotu. Saboda idan ya yi nasara a kotu, to jam’iyyar za ta ƙara ɓarkewa kenan.

Idan kuma aka tafi a haka, to an saɓule wa ɓangaren Ganduje wando a kasuwa, shi kuma Tinubu ya ɗauka. Maimakon ya ɗaura wa Ganduje, ya ɗauka a ƙugun Shekarau.

Dama masu iya magana sun ce idan kurciya za ta iya biya maka buƙata, to zabuwa ta tafi da zanen ta.