TINUBU YA ƁALLO WA KAN SA RUWA: Gwamnonin APC sun fusata da jerin sunayen dakarun rundunar yaƙin Tinubu 422, sun yi barazanar yi masa zagon-ƙasa

Gwamnonin APC sun yi barazanar yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyar zagon-ƙasa a dukkan jihohin da su ke mulki.
Gwamnonin sun fusata ne tare da zargin Tinubu ya yi fatali da sunayen waɗanda su ka damƙa masa domin a saka su cikin rundunar yaƙin neman zaɓen Tinubu 2023.
A ranar Asabar ce Sakataren Kamfen James Faleke ya bayyana sunayen mutane 422 da ke mambobin Majalisar Kamfen ɗin TInubu, cikin su har da wasu masu yawa da za su yi aiki a jihohi da yankunan su, domin ganin Tinubu da Kashim Shettima sun yi nasara a zaɓen 2023.
Kafin bayyana sunayen, sai da shugabannin jam’iyya su ka tuntuɓi Sakateriyar Ƙungiyar Gwamnonin APC (PGF), domin gwamnoni kowane ya aika da sunayen waɗanda za a saka cikin Majalisar Kamfen ɗin TInubu ɗin.
Majiya ƙwaƙƙwara ta tabbatar wa PREMIUM TIMES an nemi kowane gwamna ya bada sunayen mutum biyar.
Sai dai kuma gwamnonin sun harzuƙa, ganin yadda APC ta yi fatali da sunayen da su ka bayar, abin haushin kuma sai aka maye gurabun su da sunayen wasu daga jihohin su, ba tare da an shawarce su ba.
Wani jigon APC ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa gwamnonin su na ta kwakwazon sanar wa Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Abubakar Bagudu na Kebbi shi da Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu irin abin da aka yi masu.
An ce Gwamnan Jihar Kuros Riba Ben Ayade ya lashi takobin cewa ba zai shiga harkokin kamfen ɗin Tinubu ba. “Tunda dai shugabannin APC sun nuna masa sun fi shi sanin jihar sa.”
Gwamna Ayade ya miƙa sunayen mutanen da ya ke ganin za su iya tattara kan jama’a domin a samu ƙuri’u masu yawa a Kuros Riba, amma ba a ɗauki ko ɗaya daga cikin su ba. Ayade ya yi takarar shugaban ƙasa, amma bai yi nasara ba.
“Shi ma Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq na Kwara ya na can ya na ƙorafin cewa ya bayar da sunayen mutum biyar, amma sunan mutum ɗaya kaɗai ya gani a cikin rundunar kamfen ɗin.” Haka wani ya tabbatar, amma ya ce kada a bayyana sunan sa.
Mutumin ya sanar da wakilin mu cewa ba shi ya kamata ya yi magana da ɗan jarida ba, amma dai ya san komai ke faruwa a cikin rigimar.
“Jihar Kwara na da mutum bakwai a cikin rundunar, kuma duk daga ƙaramar hukuma ɗaya su ke.” Cewar majiyar mu.
Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo shi ma duk da an naɗa kodinatan kamfen na Shiyyar Kudu maso Yamma, ya yi kukan cewa dukkan sunayen da ya bayar ba a ɗauki ko ɗaya ba.
“Idan dai har sunayen mutum 422 ɗin da aka fitar na gaske ne ba bogi ba, to hakan na nufin APC da Bola Tinubu ba su ɗauki kamfen ɗin da muhimmanci ba.” Majiyar PREMIUM TIMES ce ta yi wannan iƙirarin.
“Mu dai abin da muka sani a jihohi gwamna ne ke da ta cewa. To idan har gwamna ya bayar da sunayen da ya ke so a saka don yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa kamfen kuma aka yi fatali da sunayen, to za a kuwa ci karo da gagarimar matsala.”
Haka ma wasu gwamnonin a Arewa na kukan cewa Tinubu ya ƙi shigar da su cikin uwar rundunar yaƙin, sai dai aka bar su da yaƙin neman zaɓen sa a jihohin su kaɗai. Saboda haka tunanin su a yanzu shi ne Tinubu bai amince da kowanen su ba, sai na jikin sa kaɗai.”
Musamman gwamnonin Arewa maso Yamma gani su ke yi makomar siyasar su na da matsala idan Tinubu ya hau mulki, domin ya mayar da su saniyar-ware.
Shi ya su yanzu sun yi amanna cewa masu kula da rundunar yaƙin neman zaɓen sa na nuna masu cewa Tinubu bai ɗauke su da wata daraja ba.
Masana wainar da ake toyawa na ganin cewa wannan wata dama ce ɗan takarar PDP Atiku Abubakar ya samu domin ya shawo kan gwamnonin Arewa maso Yamma na APC su tafi tare su tsira tare, su yi nasara tare.
Ƙoƙarin jin ta bakin Sakataren Rundunar Kamfen, James Faleke domin sanin ko za su duba ƙorafe-ƙorafe, bai yi nasara ba. An tura masa tes aka sanar da shi cewa an kira shi bai ɗauka, amma ga dalilin kiran. Har yanzu dai Faleke bai amsa ba.
Dama tun bayan fitar da sunayen an yi ta maganganu, ganin babu sunan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo a ciki.
Daga baya sai Kakakin Kamfen ɗin Rundunar Tinubu, Festus Keyamo, ya sanar wa manema labarai cewa “Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ce kada a saka sunan Osinbajo da na Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, don su maida hankalin su wajen aikin mulki, tunda Buhari ɗin ne shugaban kamfen baki ɗaya.”
Za a fara kamfen a ranar Laraba, 28 Ga Satumba.