TIKITIN MUSLIM-MUSLIM: Shugaban Ƙungiyar Dattawan ‘Arewa Ta Tsakiya’ ya caccaki APC

Shugaban Ƙungiyar Dattawan Yankin Middle Belt, Monday Morgan, ya ragargaji APC saboda ta fitar da ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakin sa duk musulmi.
Morgan wanda mamba ne na Kungiyar Kiristocin Arewa masu Adawa da Tikitin Muslim-Muslim, ya ce sun kafa ƙungiyar don yaƙi da irin wannan siyasa kawai.
Ya ce a yadda Najeriya ta ke, ba zai taɓa amincewa a yi takarar Kirista-Kirista ba, ko Muslim-Muslim.
Morgan ya ce shi ba ɗan APC ba ne, amma kungiyar su ta kafu ne biyo bayan ƙorafin da Kiristocin Arewa su ka yi, bayan APC ta zaɓi Kashim Shettima ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Ya ce duk takarar da ya ke ganin za ta tauye batu na addini, to ba ya goyon bayan ta, kuma zai yi yaƙi da ita.
Dangane da takarar APC kuwa, fitaccen ɗan siyasa Pat Utomi, ya ce ‘Tinubu tsohon kwando’ ne, Osinbajo ya fi cancanta APC ta ɗauka takarar shugaban ƙasa.
An bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed, ba shi da ƙoshin lafiyar da zai iya shugabancin Najeriya.
Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar LP, Pat Utomi ne ya bayyana haka, lokacin da ake tattaunawa da shi da Channels TV.
Utomi ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ne ya fi cancanta a ce APC ta tsaida takara, ba Tinubu ba.
Utomi ya nuna mamakin yadda Tinubu tsofai-tsofai da shi ya ke ta haƙilon lallai sai ya yi shugabancin Najeriya, maimakon ya bar Yemi Osinbajo ya tsaya wa APC takara.
“Ni dai ba zan fito ina wahala da gaganiyar neman mulki ina tsoho kamar Tinubu ba.
“Yanzu haka na sanar da ‘ya’ya na cewa idan na kai shekaru 70 kuma su ka ga ina kara-kaina da bilumbituwa, to su killace ni a gida kawai.”
Utomi ya ce Najeriya ta sha fama da rashin sa’ar shugabanni marasa lafiya, waɗanda dalili kenan Osinbajo ya fito gaba-gaɗi ya nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Ya ce Osinbajo garau ya ke, lafiyar sa ƙalau, kuma shi ya fi dacewa APC ta tsayar takara.
“Tinubu bai cancanta ba. Kai da ganin sa ka san ba shi da lafiya. Ya ce a yi masa gwaje-gwaje, kowa ya gani, kamar yadda ake yi a Amurka,” inji Utomi.
Ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da mulkin takwarkwasassun tsofaffi, mulkin da matasa ne ake cutarwa, ana maida rayuwar su marar amfani.
Utomi ya yi wannan kakkusar magana kan Tinubu, daidai lokacin da ake ta kiraye-kirayen ya janye domin ba shi da ƙoshin lafiya.
Sannan a wani gefe kuma ana sukar yadda ya dauki Musulmi kamar sa ya zama mataimakin takarar shugaban ƙasa, maimakon ya ɗauki Kirista.